Kudi Sun Rage a Asusun Kamfe, Bola Tinubu Ya Dawowa Jam’iyyar APC da N2.4m
- Kwamitin da ya taya APC yakin neman zabe a kasashen waje ya dawo da wasu kudi da suka yi saura
- Shugaban kwamitin ya ce daga cikin N10m da aka ware masu, N7.6m suka iya kashewa wajen kamfe
- Prince Ade Omole ya maidowa Jam’iyya N2m da ya yi ragowa cikin babban asusun kwamitin PCC
Abuja - Jam’iyyar APC ta karbi wasu kudi daga kwamitin da ya yi aikin tallata takarar Tinubu-Shettima a zaben shugaban kasa a kasashen ketare.
Punch ta ce kwamitin harkokin kasar wajen yakin neman zaben APC a 2023 ya dawo da Naira miliyan 2.4 zuwa ga uwar kwamitin kamfe na PCC.
Wadannan kudi sun kasance ragowar da aka bari a akawun din karamin kwamitin da aka bari da dawainiyar yi wa takarar Bola Tinubu kamfe a ketare.
Prince Ade Omole wanda shi ne shugaban kwamitin ya fitar da jawabi ranar Juma’a a garin Abuja, ya ce sun maida da N2.4m na abin da ya rage masu.
Jawabin Prince Ade Omole
Kamar yadda Mista Prince Ade Omole yake fada, wannan kudi ne ya yi ragowa a cikin Naira miliyan 10 da aka warewa jam’iyyar a lokacin zaben bana.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Bayanin kwamitin yana cikin wani zungureren rahoto mai shafi 22 da aka gabatarwa PCC.
Rahoton kudin ya shiga hannun Christopher Tarka, wanda shi ne Mataimakin Sakataren kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa watau PCC.
Dazu aka ji Omole ya yi godiya ga shugabannin PCC a madadin sauran ‘yan kwamitinsa na harkokin kasar waje kan wannan dama da suka samu.
Yana da muhimmanci a sani cewa kwamitin harkokin kasar waje ya samu N10m ne kurum a lokacin yakin neman zabe.
An ware wadannan kudi domin zirga-zirgar ‘ya ‘yan kwamitin, amma Naira miliyan 7.6 aka kashe, aka maida abin da ya rage.
- Prince Ade Omole
An yabawa kwamitin Omole
A madadin jam’iyya mai ci, Christopher Tarka ya yabi Omole da ‘yan kwamitinsa a dalilin kamanta gaskiya da rikon amana da suka nuna wajen kamfe.
Za a karasa zaben 2023
Kamar yadda rahoto ya zo a dazu, a karshen makon nan ‘yan takaran Sanatocin da ke takara a jihohin Kebbi, Sokoto da Zamfara za su san halin da suke ciki.
INEC za ta karkare zabukan da ba su kammala ba a wasu Jihohi, makomar matan Najeriya da Aisha Binani a takarar 2023 ta na hannun mutum 36, 000.
An kori Abdulmumin Jibrin
A Agustan 2019 aka ba Abdulmumin Jibrin kujera a FHA da aka kore shi daga Majalisar Wakilan Tarayya, rahoto ya zo cewa an fatattake shi daga ofis.
Bayan shekaru, Hukumar kasar ta kori ‘Dan siyasar a sakamakon bincike da aka yi a kan shi, amma Jibrin ya soki matsayar da aka dauka, ya ce ya yi murabus.
Asali: Legit.ng