Akwai Yiwuwar ‘Dan Arewa Ya Gaji Gbajabiamilla, Ya Zama Shugaban Majalisar Tarayya
- Hon. Francis Waive ya roki zababbun ‘yan majalisa su zabe shi ya zama mataimakin shugabansu
- ‘Dan siyasar na Ughelli yana so ya zama mataimakin shugaban majalisar wakilan tarayya a wannan karo
- Waive yana sa ran a bar Kudu maso kudu ta samu kujerar, ma’ana ya sallama a ba 'Yan Arewa shugabanci
Abuja - ‘Dan majalisa mai wakiltar Ughelli ta Arewa/Ughelli ta Kudu/Udu, Francis Waive zai tsaya neman takarar shugabanci a majalsa ta goma.
A ranar Alhamis, Premium Times ta kawo rahoto da ya nuna Hon. Francis Waive ya ayyana niyyar zama mataimakin shugaban majalisar wakilai.
Francis Waive ya aikawa abokan aikinsa sanarwa yana sha’awar fitowa neman takara.
Idan an yarda kujerar ta tafi bangaren Kudu maso gabas, ‘dan siyasar ya ce babu abin da zai hana sa neman mukamin a majalisar da za a rantsar.
Sakon da Francis Waive ya aika
Nayi imani majalisa ta goma ta cancanci shugabancin da zai kula da bukatun kowa sannan a hidimta ba tare da nuna bambanci ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Na yarda da daukar kowane ‘dan majalisa a matsayin daya tare da ba kowa dama a zauren majalisa da kuma rikon jagorancin kwamitoci.
Na mika kai na domin yi maku bauta a matsayin mataimakin shugabancin majalisar wakilai (idan aka kebewa yankin Kudu maso kudu)
- Hon. Francis Waive
The Nation ta ce Waive ya yi alkawarin a mulkinsa, zai tabbata an dama da kowa a majalisa, saboda haka ya nemi alfarmar zababbun ‘yan majalisa su zabe shi.
‘Dan siyasar na jihar Delta ya ce an sans hi a matsayin mutum shiru-shiru kuma mara hayaniya, yake cewa tarihinsa cike yake da yi wa al’umma hidima.
Yayin da bikin rantsar da mu ya karaso, a shirye nake in tattauna da ku mutum da mutum ko a sirri a duk lokacin da ku ke so
Da zarar kun aiko mani da sakon Whatsapp a wannan layin, sai mu yi magana. Ranar zabe kuma ka da ku manta da Francis.
- Hon. Francis Waive
Wani rahoto na This Day ya nuna zaben shugabannin majalisar wakilai ya dauki zafi, ‘yan takara daga Kudu da Arewacin Najeriya sun shirya gwabzawa.
Akwai yiwuwar a kebe matsayin ga Arewa ta tsakiya, Kudu maso kudu za su iya kawo mataimaki idan ba a ware masu shugabancin majalisar dattawa ba.
Rikicin G5 ya tashi
Nyesom Wike, Seyi Makinde, Samuel Ortom, Okezie Ikpeazu da Ifeanyi Ugwuanyi sun zama matsala a PDP, su na kokarin ganin an canza ‘yan NWC.
A gefe guda, rahoto ya zo cewa Bala Mohammed ya hada-kai da ‘yan majalisar NEC domin wargaza shirin da ‘Yan G5 ke yi wa Jam’iyyar hamayyar.
Asali: Legit.ng