Allura Ta Tono Garma: APC Ta Kawowa Kotu Hujjar da Za Ta Iya Ruguza Takarar Peter Obi
- Jam’iyyar APC ta maidawa Peter Obi martani a game da korafinsa a kan Bola Tinubu a zaben 2023
- Lauyan da yake kare jam’iyya mai mulki a kotun zabe ya ce tun asali ‘dan takarar ba ‘dan LP ba ne
- Thomas Ojo ya fadawa kotu cewa Obi ya nemi tsayawa takara a PDP, sai daga baya ya koma LP
Abuja - Jam’iyyar APC ta shigar da martaninta a kan korafin da Peter Obi ya shigar a kotun sauraron karar zaben shugaban kasa da aka yi a Fubrairu.
The Cable ta ce daya daga cikin Lauyoyin jam’iyyar APC, Thomas Ojo, ya yi fatali da karar da lauyoyin ‘dan takaran jam’iyyar LP, Peter Obi suka shigar.
A karar da ya shigar, Peter Obi ya yi ikirarin Bola Tinubu bai samu biyu bisa ukun kuri’un da aka kada a Abuja ba, yake cewa hakan sharadi ne a doka.
Lauyoyin jam’iyyar adawar ta LP sun kuma kawowa kotu zargin cewa kasar Amurka ta taba karbe $460,000 daga hannun Tinubu saboda alaka da kwayoyi.
An maidawa Obi martani
Ojo ya yi wa korafin Peter Obi raddi, yake cewa ‘dan takaran ba cikakken ‘dan jam’iyyar LP ba ne, Lauyan yake cewa har aka yi zabe, Obi ‘dan PDP ne.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jam’iyyar APC ta hannun Lauyanta ta kara da cewa har zuwa ranar 24 ga watan Mayun 2023, tsohon Gwamnan na jihar Anambra bai bar jam’iyyar PDP ba.
A watan Afrilun 2022, an tantance Obi a cikin masu neman tsayawa takarar shugaban kasa a PDP, wannan labari ya fito a jaridar Vanguard a jiya.
“Mai korafi na farko (Peter Obi) ya shiga takara kuma an tantance shi a matsayin mai neman zama shugaban kasa yayin da yake ‘dan jam’iyyar PDP
Mai korafi na farko ya yi murabus daga PDP ne a ranar 24 ga watan Mayu 2022, ya ce ya yi rajista da mai korafi na biyu (LP) a 27 ga watan Mayun 2022.
- Thomos Ojo
Yadda aka sabawa dokar zaben 2022
Rahoton ya ce jam’iyyar LP ta shirya zaben tsaida gwani ne a karshen Mayun 2022, kuma Obi ya samu nasarar da ta ci karo da sashe na 77(3) na dokar zabe.
Lauyan da ya tsayawa APC ya ce sashe na 77 na dokar zaben 2022 ya ce sai jam’iyya ta gabatarwa INEC da sunayen ‘ya ‘yanta kwanaki 30 kafin a shirya zabe.
Lauyan ya ce Obi bai da hurumin kawo kara a kan abin da ya faru kafin zabe, musamman idan aka duba cewa ta fuskar doka, bai tsaida abokin takararsa ba.
Zaben majalisar dattawa
Tun da an zabi Bola Tinubu da Kashim Shettima, an samu rahoto cewa Osita Izunaso yana burin shugaban majalisa a matsayinsa na mutumin Kudu maso gabas.
‘Dan siyasar yana so ayi la’akari da cewa bayan JTU Aguiyi Ironsi, ba a samu Ibo ya zama shugaban kasa ba, don haka yake so a amince masa ya jagoranci majalisa.
Asali: Legit.ng