Shugabancin Kasa: Muhimman Abubuwa 5 Da Ya Zama Dole Tinubu Ya Yi Don Nasara A Shugabancinsa

Shugabancin Kasa: Muhimman Abubuwa 5 Da Ya Zama Dole Tinubu Ya Yi Don Nasara A Shugabancinsa

  • Bayan sanar da dan takarar APC Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 25 ga watan Fabarairu, yanzu tsohon gwamnan Lagos din ya zama zababben shugaban kasa
  • Shugaban hukumar INEC, Mahmoud Yakubu ya ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben da aka fafata
  • A yayin da Tinubu ke shirin kama aiki a ranar 29 ga watan Mayu, akwai matsaloli biyar da dole ya fara kawo karshensu

Shugaban Hukumar INEC, Mahmoud Yakubu, ya sanar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa.

Ayyana Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa ya janyo cece-kuce a wasu sassan kasar nan. Sai dai, kasancewar kasar na fama da matsaloli da dama, kuma don samun nasarar zababben shugaban kasa, akwai bukatar a shawo kan wasu matsaloli da gaggawa.

Kara karanta wannan

Kansiloli Sun Fusata, Sun Yi Barazanar Kai Karar Abokin Takarar Peter Obi Kotu Kan Abu 1 Rak

Bola Tinubu
Abubuwa 5 Da Ya Zama Dole Tinubu Ya Yi Don Nasara A Shugabancinsa. Hoto: Bola Tinubu
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga jerin matsaloli biyar da ya kamata a magance:

1. Matsalar tsaro

Akwai matsalolin tsaro da dama da ke addabar kasar nan, wanda ke zama barazana ga sha'anin tsaro a kasar nan.

Baiwa matsalar tsaro muhimmanci. Tsare dukiya da rayukan yan kasa zai taimaka matuka wajen samar da ayyukan cigaba.

2. Magance matsalar hauhawar farashi

Najeriya na fama da matsalar tashin farashi, da yawa na fama da matsalar yanke albashi, karancin albashi ko kin biyan albashi tsawon watanni, ga kuma farashin kayan abinci na tashi. A cewar Hukumar Kididdiga ta Kasa, farashin abinci ya tashi da kaso 24.33 a watan Janairu 2023.

3. Samar da abubuwan bukatun yau da kullum

Zababben shugaban kasa ya mayar da hankali kan samarwa yan Najeriya abubuwan bukatun yau da kullum, kamar wutar lantarki da ingantaccen kiwon lafiya, idan ya kama aiki ranar 29 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Buhari Ta Zargi Peter Obi Da Cin Amanar Kasa

Tabbatar da kammala ayyukan samar da wutar lantarki a lokacin da aka yi alkawari zai taimakawa masu kasuwanci da suka dogara da wutar lantarki.

4. Cire tallafin mai

Abu daya da ke janyo koma baya ga tattalin arziki shi ne cigaba da biyan kudin tallafin mai wanda illar da yayi wa tattalin arziki ya fi amfaninsa. Farkon shekarar 2022, an ware Naira tiriliyan hudu don biyan tallafin mai, amma saboda canjin farashin mai, an kara biyan kudin da kaso 50.

5. Kara harajin Najeriya

Kara haraji zai taimaka wajen rage bashin da ake bin Najeriya da ya kai Naira tiriliyan 77.

Abin takaici, harajin da mai ke samarwa ba zai iya ciyar da kasar gaba ba. Don haka, dole shugaban kasa mai jiran gado ya samar da sabbin hanyoyin samun kudin shiga ga kasar.

Shugabancin Majalisar Dattawa: Lokaci Na Ya Yi, In Ji Orji Kalu

A wani rahoton kun ji cewa Orji Kalu, bulaliyar majalisar dattawan Najeriya ya sanar da niyyarsa na shiga jerin masu takarar shugabancin majalisar tarayyar kasa zubi na 10.

Kara karanta wannan

“Ba Za a Rantsar Da Tinubu Ba:” Magoyin Bayan Peter Obi Ya Fasa Ihu a Bidiyo, Ya Hana Jirgin Sama Tashi

Kalu mai wakiltar mazabar Abia ta Arewa a majalisar, ya fada hakan ne a ranar Talata lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a majalisar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164