Kalaman Cin Amanar Kasa: Kansiloli Sun Yi Barazanar Maka Datti Baba-Ahmed a Kotu

Kalaman Cin Amanar Kasa: Kansiloli Sun Yi Barazanar Maka Datti Baba-Ahmed a Kotu

  • Kansilolin jam'iyyar APC sun nuna rashin jin dadinsu kan furucin Datti Baba-Ahmed ya ya nemi a ki rantsar da Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu
  • Shugaban kungiyar kansilolin APC na kasa, Muslihu Yusuf Ali, ya ce abokin takarar Peter Obi makiyin damokradiyya da zaman lafiya ne
  • Sun ba Baba-Ahmed awanni 48 ya janye kalamansa ko su shigar da shi kara a kotu

Wasu kansiloli masu ci da aka zaba karkashin inuwar jam'iyyar APC sun yi barazanar daukar mataki na doka a kan Yusuf Datti Baba-Ahmed, dan takarar mataimakin shugaban kasa na Labour Party.

Yan majalisar na kananan hukumomi sun ba abokin takarar na Peter Obi wa'adin awanni 48 ya janye kalamansa kan gidan talbijin na kasa cewa kada a rantsar da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu da abokin takararsa a ranar 29 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Buhari Ta Zargi Peter Obi Da Cin Amanar Kasa

Datti Baba-Ahmed da Peter Obi
Kalaman Cin Amanar Kasa: Kansiloli Sun Yi Barazanar Maka Datti Baba-Ahmed a Kotu Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

Baba-Ahmed ya bukaci Alkalin alkalan Najeriya da kada ya rantsar da Tinubu

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa a wata hira da aka yi da Baba-Ahmed kwanan nan a gidan talbijin na kasa, ya bukaci Alkalin alkalai na Najeriya da kada ya rantsar da zababben shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hakazalika wasu magoya bayansu sun yi kira ga kafa gwamnnatin wucin gadi a kasar.

Abokin takarar Obi makiyin damokradiyya ne, kansilolin APC

Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja a jiya, shugaban kungiyar kansilolin APC na kasa, Muslihu Yusuf Ali, ya bayyana abokin takarar Obi a matsayin makiyin hadin kai, zaman lafiya da damokradiyya.

Ali ya ce:

"Za mu so yin amfani da wannan damar wajen yin Allah wadai da kalaman tunzurawa da dan takarar mataimakin shugaban kasa na Labour Party, Sanata Datti Baba-Ahmed ya yi a Channels TV a makon jiya, yana caccakar martabar zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Mataimaki Ya Fito Fili Yana Zargin Shugaban APC da Karkatar da Biliyoyin da Aka Samu

"Don haka, muna kira gare shi da ya gaggauta janye kalaman cikin awanni 48 sannan ya bai wa mutanen Najeriya masu karamci, Bola Tinubu, shugaban kasa Buhari, bangaren shari'a karkashin jagorancin Alkalin alkalan Najeriya hakuri, idan ba haka ba za a dauki matakin doka a kansa."

Yayin da yake nuna karfin gwiwar cewa za a rantsar da Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu, Ali ya bayyana Shugaba Buhari a matsayin dan damokradiyya na gaske wanda ya gudanar da zabe mafi inganci a tarihin kasar, rahoton The Guardian.

Dun wanda bai gamsu ba ya tafi kotu, Buhari ga wadanda suka fadi zaben 2023

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake kira ga yan takarar da suka sha kaye a zaben 2023 da su garzaya kotu idan har basu gamsu da sakamakon zaben ba.

Buhari ya kuma yi kira ga Atiku Abubakar, Peter Obi da sauransu da su yi hakuri su ba bangaren shari'a damar yin aikinsu a tsanaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng