An Samu Wanda Ya Fito Takarar Shugaban Majalisa, Ya Ziyarci Gwamnoni 24 a Boye
- ‘Dan Majalisar APC ya fito neman shugabancin majalisa ta goma, yana kamfe ta bayan fage
- Hon. Yusuf Gagdi zai kawowa Idris Wase cikas wajen rike majalisar wakilan tarayya a 2023
- Gagdi ya na wakiltar mazabar Pankshin-Kanke-Kanam daga jihar Filato a APC mai rinjaye
Abuja - Yusuf Gagdi yana cikin wadanda suka fito neman kujerar shugaban majalisar wakilan tarayya a Najeriya, da alama ba da wasa ya fito ba.
Premium Times ta ce zuwa yanzu Honarabul Yusuf Gagdi ya gana da Gwamnoni 24 daga cikin Gwamnonin jihohi 36 da ake da su a fadin kasar nan.
Kokarin da ‘dan majalisar yake yi shi ne samun goyon bayansu a takarar da yake yi a APC.
Da ya zanta da manema labarai a ranar Laraba, Gagdi mai wakiltar Pankshin, Kanke da Kanam, ya ce yana bi a sannu domin samun goyon baya.
Mulkin Tinubu: Jiga-jigan 'Yan Siyasa 3 Sun Hada Kai, Sun Fadi Wanda Suke So Ya Zama Shugaban Majalisa
Sannu a hankali ake kamfe
Rahoton ya ce ‘Dan majalisar ya nuna a boye shi da mutanensa su ke aiki domin ganin ya yi nasarar zama sabon shugaban majalisar wakilai.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Baya ga gwamnonin da ke ofis, Gagdi ya ce ya zauna da Gwamna mai-jiran gado a jihar Abia watau Olex Otti wanda ya lashe zaben a karkashin LP.
Hon. Gagdi yana bin 'Yan LP
Gagdi ya zauna da Otti a Legas ne domin samun goyon bayan ‘ya ‘yan jam’iyyar LP da za su je majalisa. Haka zalika ya yi zama da Chijioke Edeoga.
Bayan zaman da ya yi da Chijioke Edeoga wanda ya nemi takarar Gwamna a zaben 2023, sai ya wuce wajen shugaban LP na reshen jihar Enugu.
Tribune ta rahoto Gagdi yana bayanin muhimmancin shawo kan jam’iyyar LP wanda za ta samu ‘ya ‘ya da-dama a majalisa ta goma da za a rantsar.
‘Dan majalisar na APC ya ce a boye ya ziyarci Gwamnoni 24 da ke kan mulki, ya ki ambatar sunayensu domin kuwa ya ce shi a boye yake yakinsa.
"Za a ga gyara a Majalisa"
Idan Gagdi ya zama shugaban majalisar wakilai, Punch ta ce ya yi alkawarin kawo karshen mai-mai da ake da samu na kwangilolin gwamnati.
Burinsa ne a samu gyara a kundin kasafin kudin Najeriya, a daina facaka da dukiyar al’umma.
Canji a Jam’iyyar NNPP
Labarin da mu ka samu a daren Juma’a shi ne daya daga cikin mataimakan Farfesa Rufai Ahmed Alkali aka dauko ya gaje shi a Jam’iyyar NNPP.
Abba Kawu-Ali zai jagoranci NNPP mai alamar kayan dadi a Najeriya. Kafin samun wannan mukami, shi ne shugaba daga Arewa maso gabas.
Asali: Legit.ng