Zan Yi Nesa da Abuja Bayan 29 Ga Watan Mayu, 2023, Inji Shugaba Buhari
- Shugaban Najeriya, Alhaji Muhammadu Buhari, ya ce zai raba kansa da Abuja da zaran ya miƙa mulki ranar 29 ga watan Mayu, 2023
- Buhari ya kuma yaba wa kwamishinar Burtaniya a Najeriya da zata tafi cewa danƙon alakar tsakanin kasashen biyu zata kara karfi
- Ta ce tana takaicin barin Najeriya saboda ta shaƙu sosai da abubuwa da dama amma wata rana zata dawo
Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ce ya ƙagara ya yi ritaya zuwa Daura, jihar Katsina, bayan miƙa mulki ga sabon shugaban ƙasa ranar 29 ga watan Mayu, 2023.
Shugaba Muhammadu Buhari ya faɗi haka ne a fadarsa da ke Abuja yayin da ya karbi bakuncin kwamishinar Burtaniya a Najeriya mai barin gado, Catriona Wendy Laing, ranar Laraba.
Daily Trust tace a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ya fitar, shugaba Buhari, ya ce, "Zan nesanta kaina da Abuja iyakar iyawata."
Bayan haka ya yaba wa ƙasar Burtaniya bisa haɗin kan da take baiwa gwamnatin Najeriya a bangarori da dama musamman kokarin sake gina arewa maso gabas, wanda ta'addanci ya ɗaiɗaita.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Buhari ya bayyana cewa ƙasar Burtaniya ta kasance gida na biyu a wurin wasu 'yan Najeeiya kuma kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin kasashen biyu zata ci gaba da ƙara ƙarfi.
"Maganar gaskiya wasu masu arziƙi a Najeriya ba su jin daidai har sai sun mallaki gida a ƙasar Burtaniya," inji shugaban kasa Buhari.
Ina kaunar Najeriya - Laing
Tun da fari, Laing, ta ce tana takaicin barin Najeriya domin jininta ya riga ya shaƙu matuƙa da rayuwa a ƙasar nan musamman kaɗe-kaɗe, rawa da al'adu.
"Ina takaicin barin Najeriya, akwai nishaɗi sosai a Najeriya, na mori lokacina a nan ba zan manta ba kuma wata rana zan dawo. Ina son raye-raye, kaɗe-kaɗe da al'adun kasar nan."
"Na samu tulin ilimi a Najeriya, na shiga kasashe sama da 20 kuma na faɗa wa wadanda zasu gaje ni su kwaikwayi abinda na yi. Zan dawo kuma na ƙara yawo sosai."
Ta kuma taya shugaba Buhari murnar kammala zangon mulkinsa 2 na shekaru 8, inda ta ce ya yi iya kokarinsa bakin rai bakin fama wajen tabbatar da haɗin kan ƙasa.
Gwamnan Abiya Ya Nada Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnatinsa
A wani labarin kuma Watanni ƙasa da 2 gabanin miƙa mulki, Gwamna Ikpeazu ya ci gaba da naɗe-naɗe a gwamnatinsa
Gwamnan na jihar Abiya, mamban G5 dake cikin PDP, ya naɗa sabon shugaban ma'aikatan gidan gwamnatinsa kuma ya ce naɗin zai fara aiki nan take.
Asali: Legit.ng