APC da Mambobi Majalisa Na Goyon Bayan Wase Ya Zama Kakakin Majalisa, Buni
- Gwamna Mala Buni na jihar Yobe ya tabbatar da goyon bayansa ga kudirin Idris Wase na zama kakakin majalisar wakilai
- Buni, tsohon shugaban kwamitin rikon kwarya na APC ta kasa ya ce lokaci ya yi da za'a saka masa bisa biyayyar da ya nuna a baya
- Ahmed Idris Wase na ɗaya daga cikin masu takarar kujerar shugaban majalisar wakilan tarayya ta 10
Abuja - Tsohon shugaban APC na rikon kwarya kuma gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ya nuna goyon bayansa ga mataimakin kakakin majalisar wakilai, Ahmed Idris Wase.
Vanguard ta ce gwamna Buni ya bayyana cikakken goyon bayansa ga Wase a yunkurinsa na zama kakakin majlisar wakilai ta 10 da za'a rantsar nan gaba.
Mala Buni ya bayyana matsayarsa kan shugabancin majalisar yayin da Wase da 'yan tawagarsa suka ziyarce shi a gidansa na Abuja.
Mulkin Tinubu: Jiga-jigan 'Yan Siyasa 3 Sun Hada Kai, Sun Fadi Wanda Suke So Ya Zama Shugaban Majalisa
A kalamansa ga Ahmed Wase, gwamna Buni ya ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Mu a cikin APC da kuma majalisar wakilan tarayya kanta mun fi buƙatarka fiye da yadda kai kake buƙatarmu saboda ina ganin ba bu wani lokaci da ya kamata jam'iyya ta saka maka bisa biyayyarka kamar yanzu."
"Ita kwarewa a fannin aiki ba a jami'a ake koyo ba, ta ƙunshi shiga a dama da kai a hukuma da kuma sanin dabaru wanda munsan ka tara su. Mu dai mun san zaka yi aiki da kwarewa saboda ka shirya tsaf."
"Ba bukatar sai ka kawo mun ziyara, zan mara maka baya saboda iya zubinka iya abinda zaka kwasa. Ka ji maganarmu kuma ka janye lokacin ina Sakataren na kasa, lokaci ya yi da zamu maida biki."
Gwamna Buni ya kara da cewa kamar yadda Wase ya janye wa wani a baya, ya zama wajibi a yanzu ya girbi abinda ya shuka, wani ya jnage masa kamar yadda ya yi.
Gwamnonin da suka fara shiga matsala tun kafin sauka daga mulki
A wani labarin kuma mun tattara muku Jerin Sunayen Gwamnonin da Suka Fara Takun Saƙa da Waɗanda Zasu Gaje Su Tun Kafin Miƙa Mulki
Gwamna Ganduje na jihar Kano na ɗaya daga cikin waɗan nan gwamnon kuma a halin yanzun yake musayar yawu da Abba Gida-Gida.
Asali: Legit.ng