Babbar Kotu Ta Dakatar da Shugaban LP da Wasu Jiga-Jigai Uku

Babbar Kotu Ta Dakatar da Shugaban LP da Wasu Jiga-Jigai Uku

  • Babbar Kotu a birnin tarayya Abuja ta dakatar da shugaban Labour Party na kasa, Sakatare da wasu shugabanni 2
  • Kotun ta haramta musu ayyana kansu a matsayin masu rike da kujerun jam'iyya na kasa bisa zargin da ake musu
  • Wannan na zuwa ne makonni bayan jam'iyyar PDP ta shiga makamancin wannan matsalar

Abuja - Babbar Kotun birnin Abuja ta ba da umarnin haramta wa shugaban Labour Party, Julius Abure, da Sakatare, Farouk Ibrahim da wasu 2 bayyana kansu a matsayin shugabannin jam'iyyar na ƙasa.

Channels tv ta tattaro cewa sauran waɗanda Kotun ta dakatar daga ayyana kansu a matsyain shugabanni LP na kasa su ne, Sakataren tsare-tsare, Clement Ojukwu, da ma'ajiyi, Oluchi Opara.

Shugaban LP na ƙasa, Julius Abure.
Babbar Kotu Ta Dakatar da Shugaban LP da Wasu Jiga-Jigai Uku Hoto: Labour Party
Asali: Facebook

Mai shari'a Hamza Mu'azu ne ya sanar da wannan umarnin yayin da yake yanke hukunci kan wata ƙara da James Onoja ya shigar gaban Kotu.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 3 da Suka Auka Matsalar Zabe Bayan Yin Fito Na Fito da Buhari a Kan Canjin Kudi

Meyasa Kotu ta dauki wanna matakin?

A zaman shari'ar, Mista Onoja ya gaya wa Kotu yadda dakatattun shugabannin suka kirkiri takardar babbar kotun Abuja ta karya domin su sauya sunayen yan takara a babban zaɓen 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daga cikin takardun Kotun da suka kwaikwaya suka yi na ƙarya don cimma burinsu har da takardar shaida Rasiɗi, kwacewa da maye gurbi.

Babban lauyan ya gabatar da kalar takardun domin tabbatarwa Alƙali cewa babban Rijistaran Kotu ya ankarar da LP ɗanyen aikin da su Abure da sauransu ke aikatawa.

Ya rubuta wasiƙa zuwa ga Labour Party ya nemi ta nesanta kanta daga takardun da aka yi amfani da su wajen aikata muggan laifuka da sahalewar Abure da sauran mutane uku.

Hukuncin da Kotu ta yanke

A wani takaitaccen hukunci, mai shari'a Mu'azu ya ce ƙarar da kuma takardun da suka mara mata baya sun isa su gamsar da Kotu ta amince da buƙatun mai ƙara.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: 'Yan Sanda Sun Mamaye Babbar Sakatariyar Jam'iyya, Sun Kwace Iko Da Ita

Bayan nan ne Alkalin ya umarci cewa mutanen huɗu su daina nuna kansu a matsayin masu rike da kujerun shugabannin Labour Party a matakin ƙasa, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Rikicin PDP ya tsananta

A wani labarin kuma APC Ta Dakatar da Shugaban Jam'iyya da Babban Jigo Kan Cin amana da zagon ƙasa

Bugu da ƙari jam'iyyar ta nesanta kanta daga wasu kalamai da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya yi game da alaƙar Bola Tinubu da shugaban INEC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262