Sanatan APC Ya Yi Kus-Kus da Buhari a Aso Villa, Ya ce Zai Zama Shugaban Majalisa
- Osita Izunaso ya ce ya cancanta ya zama shugaban majalisar dattawa da za a rantsar a watan Yuni
- Gogaggen ‘dan siyasar ya ce bai da sa’a a cikin Sanatocin Kudu maso kudu da Kudu maso gabas
- Idan APC ta ce a fito da shugaban majalisa daga Kudu maso gabas, Izunaso yana ganin shi ne a gaba
Abuja - Osita Izunaso wanda zai wakilci Imo ta yamma ya yi wani zama da shugaba Muhammadu Buhari a fadar shugaban Najeriya a yammacin Talata.
Jim kadan bayan ya hadu da Mai girma shugaban kasa, Premium Times ta rahoto Osita Izunaso yana cewa ya cancanci ya jagoranci majalisar dattawa.
Zababben Sanatan yana cikin masu neman shugabancin majalisa ta goma, ya shaidawa manema labarai cewa ya cancanci ya rike wannan mukami.
A cewar ‘dan siyasar, adalci shi ne a kebe shugabancin majalisar dattawa zuwa ga yankin Kudu maso gabas. Idan aka yi haka, damar Izunaso za ta karu.
Rahoton ya ce Izunaso ya fara zama ‘dan majalisar wakilai ne kafin ya samu karin matsayi zuwa majalisar dattawa, don haka yake ganin ya san kan aiki.
Da aka tambayi zababben ‘dan majalisar game da yadda yake ganin cin ta, sai ya ce ya sha gaban sauran masu harin kujerar domin ya fi su dadewa a ofis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
The Cable ta rahoto Izunaso yana mai cewa a cikin kaf yankin Sanatocin Kudu maso gabas da na Kudu maso kudu, babu wanda ya dade a majalisa kamarsa.
"A zahiri yake, a duk fadin Kudu maso kudu da Kudu maso gabas, na fi kowa tsufa. Babu Sanata a jam’iyyar APC da ya fi ni dadewa, kuma dadewa ke amfani.
Na zo majalisar dattawa a 2007, na je majalisar wakilai, nayi shekaru biyar a jam’iyya. Na rike kujerar Sakataren gudanarwa daidai gwagwado karfina."
- Osita Izunaso
Abokan takarar Izunaso
Takarar ‘dan majalisar za ta fuskanci kalubale daga Muhammad Sani Musa (APC, Neja), Dave Umahi (APC, Ebonyi), da kuma Orji Uzor Kalu (APC, Abia).
Ana da labari Abdulaziz Yari (APC, Zamfara) da Barau Jibrin (APC, Kano) su na neman kujerar, akwai alamun Aliyu Wamakko (APC, Sokoto) zai bi sahu.
Asali: Legit.ng