Mataimaki Ya Fito Fili Yana Zargin Shugaban APC da Karkatar da Biliyoyin da Aka Samu

Mataimaki Ya Fito Fili Yana Zargin Shugaban APC da Karkatar da Biliyoyin da Aka Samu

  • Salihu Lukman ya cigaba da jifan shugaban jam’iyyar APC na kasa da laifin rashin gaskiya a NWC
  • Mataimakin shugaban jam’iyyar na APC ya ce Abdullahi Adamu ya ki yin bayani a kan harkar kudi
  • APC ta samu kudi masu yawa ta hanyar saida fam din shiga zabe, Lukman ya ce an bar abin a duhu

Abuja - Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso yamma, Salihu Lukman ya bukaci Abdullahi Adamu ya dawo da wasu kudi.

The Cable ta ce Salihu Lukman ya na so shugaban APC na kasa ya maido biliyoyin kudin da jam’iyya ta samu wajen saida fam din shiga takara.

Jam’iyyar APC mai ci ta saida takardar neman shiga takarar shugaban kasa ga mutane akalla 20, an saida kowane fam a Naira miliyan 100.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Gwamna Wike Bai Hakura Ba, Ya Kara Dauko Hanyar Ruguza Jam'iyyar PDP

Baya ga haka, APC ta samu kudi masu yawa daga saida fam din shiga zaben Gwamna, majalisar wakilai da dattawa da na majalisar dokoki.

Lambar Adamu Iyiola Omisore ya fito

A wani rubutu da ya fitar a ranar Litinin, Lukman ya fito yana cewa Adamu da Iyiola Omisore su ka rika daukar duk matakin da ya shafi harkar kudi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanata Iyiola Omisore shi ne Sakataren APC na kasa, Lukman yana cikin mataimakan Adamu a NWC, amma akwai rashin jituwa tsakaninsu.

Shugabannin APC
Jagororin APC a Legas Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Sauran 'Yan NWC ba su da amfani

Shugaban na APC mai wakiltar Jihohi bakwai na Arewa maso yamma a majalisar gudanarwa ta kasa ya zargi abokan aikinsa da zama ‘yan amshin shata.

Zargin da ‘dan siyasar yake yi shi ne shugabannin da ke kula da NWC sun shiga hurumin majalisar koli ta NEC, su na batar da kudi ba tare da bin doka ba.

Kara karanta wannan

Bayan Korar Shugaban PDP, Wike Ya Fallasa Facakar Biliyoyin da Aka Yi a 'Yan Watanni

An yi watsi da aikin majalisar NEC wanda ya hada da amincewa da kasafin kudin jam’iyya kamar yadda ya zo a sashe na 13.3A(xiv) na dokar jam’iyya.
Sannan sashe na 13.3A(xv) na kundin tsarin jam’iyya ya umarci majalisar NWC ta rika ba NEC rahoton kudin da aka kashe duk bayan watanni hudu.
Sashen 13.4(iv) ya tursasawa NWC gabatar da rahoto a kan kudin da aka samu da yadda aka kashe su, duk da haka, an yi watsi da wadannan abubuwa.

Kamar yadda wani rahoto ya nuna, har zuwa yau, Lukman ya ce NWC ba ta fadi abin da ta gada a cikin asusu daga hannun kwamitin riko na Mai Mala ba.

...An sallami Ovie Omo Agege

Ku na da labari cewa wasu shugabannin jam'iyyar APC na reshen Delta sun kori 'Dan takarar Gwamna, Ovie Omo Agege da zargin ya yi zagon kasa a zabe.

Amma NWC ta ce babu wannan magana domin ba ta san da zaman 'yan tawaren da suka dauki wannan mataki ba, wanan shi ne matsayar 'dan takarar.

Kara karanta wannan

To fah: Mataimakin shugaban APC ya fadi yankin da ya kamata a ba kujerar Ahmad Lawal

Asali: Legit.ng

Online view pixel