An Gano Sunayen Mutum 3 da Tinubu Ke Shirin Ba Manyan Muƙamai

An Gano Sunayen Mutum 3 da Tinubu Ke Shirin Ba Manyan Muƙamai

  • Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, na kan gaba wajen maye gurbin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa
  • Wasu majiyoyi sun ce shugaban kasa mai jiran gado, Bola Tinubu, ya riga ya rubuta tawagarsa da zai kafa gwamnati da su
  • Haka nan an gano cewa Tinubu ya gama yanke tawagar tattalin arziki, inda aka hangi sunayen jiga-jigai a sahun gaba

Rahotannin da ke fitowa a halin yanzu sun nuna cewa zaɓaɓɓen shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, na shirin naɗa kakakin majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila, a babban matsayin da zaran ya karɓi mulki.

Bayanan sun nuna cewa Tinubu na shirin gwangwaje Gbajabiamila da muƙamin shugaban ma'aikatan fadarsa idan aka rantsar da shi ranar Litinin, 29 ga watan Mayu, 2023.

Femi, Tinubu da Bagudu.
An Gano Sunayen Mutum 3 da Tinubu Ke Shirin Ba Manyan Muƙamai Hoto: Femi Gabajabiamila, Bola Tinubu da Atiku Bagudu
Asali: Facebook

Rahoton This Day ya ce, manyan mutane kamar Wale Edun, tsohon kwamishinan kuɗi a jihar Legas da kuma gwamnan jihar Kebbi mai ci, Atiku Bagudu, na cikin jerin sunayen da Tinubu ya ware wa babban muƙami.

Kara karanta wannan

Mazan jiya: Hotunan gidan Tafawa Balewa sun jawo martani mai daukar hankali a intanet

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa sunayen Mista Edun da Atiku Bagudu, sun fita a cikin tawagar ɓangaren tattalin arziki a gwamnatin Tinubu yayin da ake tunkarar bikin rantsarwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata majiya ta ce:

"Da yuwuwar Wale ne zai zama jagoran bangaren tattalin arziki, ko dai Ministan kuɗi ko kuma gwamnan babban bankin Najeriya (CBN). Har yanzun bamu da taƙamaiman shirin Tinubu kan Bagudu."
"Amma yana cikin waɗanda sunansu ya shiga ciki kuma zai ja ragamar babban ɓangare mai matuƙar muhimmanci a gwamnati mai kama wa."

Idan zaku iya tunawa, Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Gbajabiamila na hanyar zama shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin tarayyan Najeriya na gaba.

Wata majiya ta daban da ta yi tsokaci kan wannan labarin, ta ce:

"Idan kuka tuna, bai karɓi shaidar cin zaɓe ba ranar Laraba, ba ya buƙatar Satifiket ɗin INEC, yana da duk abinda ya kamata na aiki a matsayin shugaban ma'aikatan shugaban kasa a sabuwar gwamnati."

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Buɗe Wuta, Sun Kashe Mutane Akalla 15 Ana Tsaka da Sallah a Masallaci

Ganduje Ya Fusata da Kalaman Abba Gida-Gida

A wani labarin kuma Gwamna Ganduje Ya Fusata, Ya Maida Zazzafan Martani Ga Abba Gida-Gida Kan Karɓo Bashi

Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya caccaki gwamna mai jiran gado da shiga sharo ba shanu tamkar shi ne gwamna mai ci.

Ganduje ya ce kalaman da Abba Kabir Yusuf ke saki a baya-bayan nan alama ce ta rashin sanin shugabanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262