"Mara Amfani" Ganduje Ya Fusata da Kalaman Abba Gida-Gida Na Hana Shi Bashi

"Mara Amfani" Ganduje Ya Fusata da Kalaman Abba Gida-Gida Na Hana Shi Bashi

  • Gwamnan Kano ya fusata da kalaman Abba Gida-Gida, ya ce maganganun da yake alama ce ta rashin sanin shugabanci
  • Dakata Abdullahi Ganduje ya ce shawarin da zababben gwamnan yake bayarwa ba su da amfani
  • Wannan na zuwa bayan sabon gwamnan ya gargaɗi masu baiwa gwamnatin Kano bashi su dakata

Kano - Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya caccaki zaɓaɓɓen gwamna, Abba Kabir Yusuf, bisa kalaman da ya yi a baya-bayan nan kan ciyo bashi.

Ganduje ya kira kalaman gwamna mai jiran gadon da, "Mara tushe" da kuma alama ce dake nuna bai san inda ya dosa ba, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

Abba da Ganduje.
Abba Gida-Gida da Gwamna Ganduje Hoto: channelstv
Asali: UGC

Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida ya shawarci masu baiwa gwamnatin Ganduje Bashi su dakata kuma ya gargaɗi masu gini a filayen gwamnati su shiga taitayinsu.

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida: Ba Zan Biya Duk Wani Bashi Da Ganduje Ya Ciwo Wa Kano Bayan Zabe Ba

Ganduje ya maida martani

Ganduje ya yi martani kan kalaman ne yayin da yake jawabi ga manema labarai ranar Asabar jim kaɗan bayan kammala taron Addu'o'i da rokon Allah ya taimaki shugaban masa mai jiran gado, Bola Tinubu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce:

"Wannan babbar alama ce a zahiri da ke nuna shugabancinsu ba shi da manufa saboda irin waɗannan shawarin ba su da amfani kuma ba su da tushe."
"Yana magana da jiji da kai kamar yanzu haka shi ne gwamna Kano. Muna masa fatan ya yi abun kirki amma abinda muke so ka gane zamu kalubalanci wannan nasarar ta wucin gadi a Kotun sauraron karar zaɓe."
"Amma ka ga mutum ya fara magana barkatai irin waɗan nan, ai kai zaka wa kanka alkalancin cewa bai fara da kafar dama ba."

Kara karanta wannan

Sarki 2 a Zamani 1: Har Gobe Ni Ne Gwamnan Kano – Dr. Ganduje ga Abba Gida Gida

Abba Gida-Gida ya fara magana kan harkokin gwamnatin Kano mako ɗaya bayan INEC ta ce shi ne ya lashe zaɓen ranar 18 ga watan Maris, 2023, wanda Ganduje yace a haɗu a Kotu.

Yadda zan kawo karshen ta'addanci a Katsina - Dikko Raɗda

A wani labarin kuma Zababben Gwamna Zai Bullo Da Sabuwar Dabarar Yakar Yan Ta'adda a Katsina

Gwamna mai jiran gado a jihar Katsina, Dakta Dikko Umaru Radda, ya sha alwashin sharewa Katsinawa hawayensu na tsawon shekaru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel