Gwamna Ganduje Ya Sake Dura a Kan Abba, Zababben Gwamna Ya Maida Masa Martani
- Abdullahi Umar Ganduje ya ce azarbabin Abba Kabir Yusuf ya nuna bai san inda ya dosa ba
- Gwamnan jihar Kano ya shaidawa manema labarai cewa za su karbe nasarar da NNPP ta samu
- Ganduje bai jin dadin katsalandan da Abba yake yi masa tun kafin ya karbi mulkin Kano
Kano - Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya zargi Abba Kabir Yusuf da farawa babu BismilLah, bayan nasarar da ya samu a zabe.
A wani bidiyo da Abubakar Aminu Ibrahim ya wallafa a shafinsa na Facebook, an ji Dr. Abdullahi Umar Ganduje yana sukar Abba Kabir Yusuf.
Mai girma Gwamnan ya zargi Abba Kabir Yusuf da yin kalamai tamkar wanda ya zama Gwamna, ya na mai kara tuna masa bai shiga ofis ba.
Gwamna Ganduje yake cewa su na yi wa Abba addu’ar ya yi mulki da kyau, amma duk da haka za su kalubalanci nasararsa a gaban kotun zabe.
An fara samun rashin jituwa
Daily Trust ta ce ana samun sabani tsakanin Gwamna Ganduje da Abba Gida-Gida ne bayan zababen Gwamnan ya rika fitar da wasu sanarwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake jawabi ga ‘yan jarida bayan taron addu’o’i da aka shiryawa Bola Tinubu a gidan gwamnati, Ganduje ya ce Abba ya nuna sam bi da saiti.
Jawabin Mai girma Gwamna
Alama ce karara cewa shugabancinsu bai da alkibla domin kuwa shawarwarin da yake badawa ba su da tushe.
Ya na yin magana tamkar shi ne Mai girma Gwamnan jihar Kano a yanzu. Bai zama Gwamna ba har yanzu tukuna.
Mu na yi masa addu’ar sa’a, amma abin da muke fada masa shi ne za mu kalubalanci gajerar nasarsa a kotun zabe.
Sannan mutum ya fara fitar da jawabai irin wannan, za ku iya zama Alkalai cewa ya shigo mulki da kafar hagu.
Martanin Abba Kabir Yusuf
Legit.ng ta saurari Abba Yusuf a bidiyo, yana kare kan shi, yana cewa zai cigaba da bada wadannan shawarwari duk da abin da Gwamna yake fada.
Gwamna mai jiran gado ya zargi Gwamnatin APC mai barin ofis da daukar ma’aikata fiye da 1, 500 aiki a ‘yan kwanakin nan saboda a bar shi da aiki.
Rantsar da sabon Shugaban Kasa
Rahoto ya zo cewa an sake samun Jam’iyyar adawar da ta kalubalanci nasarar Bola Tinubu a kotun zabe. Lauyan All Peoples Movement (APM) ya shigar da kara.
APM ta nemi kotun karar zabe ta ruguza nasarar da Bola Tinubu ya samu saboda Kashim Shettima ya shiga takarar Shugaban kasa da na Majalisa a lokaci daya.
Asali: Legit.ng