Zababben Gwamna Zai Bullo Da Sabuwar Dabarar Yakar Yan Ta'adda a Katsina

Zababben Gwamna Zai Bullo Da Sabuwar Dabarar Yakar Yan Ta'adda a Katsina

  • Zababben gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya ziyarci shugaba Muhammadu Buhari, a fadarsa da ke Abuja
  • Bayan ganawarsu, Radɗa ya sha alwashin kawo karshen ta'addanci da zaran ya shiga Ofis a watan Mayu
  • Gwamna Masari ne ya yi wa sabon gwamnan jagora domin nuna wa Buhari shaidar cin zaɓe da INEC ta ba shi

Abuja - Sabon gwamnan jihar Katsina mai jiran gado, Dikko Umaru Raɗɗa, ya sha alwashin amfani da fasahar zamani wajen magance ta'addanci a faɗin jihar.

Dakta Radda, ya kuma lashi takobin magance matsalar tsaro ta yadsa manoma zasu samu natsuwar ci gaba da zuwa gonakinsu da zaran ya karɓi mulki a watan Mayu.

Masari da Radda sun je wurin Buhari.
Lokacin da Masari ya jagoranci Dikko Radda zuwa wurin Buhari Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Zababben gwamnan ya faɗi haka ne yayin zantawa da masu ɗauko rahoto daga gidan gwamnati jim kaɗan bayan ganawa da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Ko "Diris" Ba Zan Saka Hannu Na a Cikin Gwamantin Kano Mai Zuwa Ba - Kwankwaso

Channels tv ta rahoto cewa Radda ya ziyarci shugaba Muhammadu Buhari ne domin nuna masa shaidar cin zaɓe da hukumar INEC ta damƙa masa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sabon gwamnan ya sake ɗaukar alƙawarin cewa zai dawo da harkokin noma gadan-gadan a matsayin hanyar farfaɗo da tattalin arziƙin jihar da ke arewa maso yamma.

Dikko Raɗɗa ya ziyarci shugaban kasa Buhari, wanda ɗan asalin jihar Katsina ne bisa jagorancin gwamna mai ci, Aminu Bello Masari.

Tsohon shugaban SMEDAN din ya ƙara da cewa tuni ya kaddamar da kwamitin da zai sake nazari kan tsaruka da dabarun gwamnati mai ci.

Ya ce duk shawarwarin da kwamitin ya gabatar zai aiwatar da su bayan ranar 29 ga watan Mayu, 2023, idan ya karɓi shahadar kama aiki a matsayin gwamna.

INEC ta ayyana Raɗɗa na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna jihar Katsina wanda ya gudana ranar 18 ga watan Maris, 2023, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Zabaɓben Gwamnan APC a Jihar Sakkwato Ya Roki Tambuwal, PDP da Wasu Mutane Abu 1

Wani mamban APC a Katsina, Lawal Yahuza, ya shaida wa Legit.ng Hausa cewa suna kyautata zaton sabon gwamna zai yi abinda ya dace duba da maganganun da yake yi.

Ya ce:

"Muna wa sabon gwamna mai jiran gado fatan Alheri, Allah ya ba shi ikon cika waɗan nan alkawurra da ya ɗauka. Tabbas idan ya magance ta'addanci, Katsina zata samu ci gaba sosai."

Haka nan wakilinmu ya zanta da wani mazaunin Katsina, Zaharaddini Khamisu, ya ce alamu sun nuna duk da basu zaɓi Radɗa ba zai zame wa Katsinawa Alheri.

Ya ce ya saurari hirar da ya yi bayan ganawa da Buhari, "Ina ganin idan Radɗa ya samu masahawarta na gari, zai iya kawo ƙarshen hawayen 'yan Katsina kuma noma zai farfaɗo."

Minista man fetur ya yi murabus kan abu ɗaya

A wani labarin kuma Hadimin Shugaban Kasa Yace Ministan Buhari Ya Yi Murabus, Ya Faɗi Sunansa da Dalili

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan 2023: Taya Murnar Nasir Yusuf Gawuna Ga Abba Kabir Yusuf Gida-Gida

Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa ya tabbatar da labarin cewa karamin ministan albarkatun man fetur, Temipre Sylva, ya yi murabus daga kan muƙaminsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262