Sarki 2 a Zamani 1: Har Gobe Ni Ne Gwamnan Kano – Dr. Ganduje ga Abba Gida Gida
- Abdullahi Umar Ganduje ya yi raddi ga shawarar da Abba Kabir Yusuf ya fito ya ba al’umma
- Gwamnan ya ce har yanzu shi yake da gwamnati muddin ranar 29 ga watan Mayu ba tayi ba
- Ganduje ya fadawa Abba Kabir Yusuf cewa ba shi ya fara saida filayen jama’a a Kano ba
Kano - Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya yi kira ga Abba Kabir Yusuf wanda zai karbi mulki a hannunsa a ranar 29 ga watan Mayu.
Rahoto ya fito daga Daily Trust a yammacin Alhamis cewa Abdullahi Umar Ganduje ya maida martani ga jawabin da Abba Kabir Yusuf ya fitar a jiya.
Mai girma Gwamnan ya fitar da jawabi ta hannun Kwamishinan yada labarai da kuma harkokin cikin gida, Muhammad Garba a yammacin Juma’a.
Malam Muhammad Garba ya bukaci zababben Gwamnan wanda aka fi sani da Abba Gida Gida ya guji fitar da sanarwa domin gudun ya jawo rudani.
Shawarar Abba Kabir Yusuf
Shi dai Abba Yusuf ya fitar da sanarwa yana bada shawara ga wadanda suka saye filaye a kadarorin gwamnati da su dakata da ginin da suka dauko.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kwashinan labaran ya tunatar da Abba mai shirin hawa gadon-mulki cewa har zuwa yanzu, wa’adin Gwamnati Abdullahi Ganduje bai kare ba tukuna.
Martanin Gwamnan Kano
"Abin da gwamnan ya yi na bada umarni a kan sha’anin gwamnati yayin da wa’adin wanda yake ofis bai kare ba, zai zama riga-malam masallaci.
Ganduje ne Gwamna mai cikakken ido har zuwa ranar 29 ga watan Mayu kuma yana da damar da zai gudanar da aikinsa la’akari da kishin al’umma.
Har sai ya yi rantsuwar zama Gwamna a ranar 29 ga Mayu, amma a yanzu shi ba komai ba ne illa zababben Gwamna wanda bai dauke da wani iko.
Abin da zai iya shi ne ya soke wasu matakan da wanda ya gabace shi ya dauka idan ya shiga ofis, idan akwai bukatar hakan, yanzu bai da iko a doka.
- Malam Muhammad Garba
Aminiya ta rahoto Muhammad Garba yana cewa ko ana daren barin ofis ne, Ganduje ne yake da wuka da nama kamar yadda ya dauki rantsuwa a 2019.
Kwamitin karbar mulki
Dazu aka samu labari Dr. Abdullahi Baffa Bichi aka zaba a matsayin shugaban kwamitin mutum 65 da zai yi shirin karbar mulki a jihar Kano.
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da kwararren Litikan nan, Aminu Magashi su na cikin kwamitin karbar mulki tare da irinsu Farfesa Hafizu Abubakar.
Asali: Legit.ng