An Fara Diraman Bayan Zabe A LP Yayin Da Jam'iyyar Ta Dakatar Da Jiga-Jiganta 11 A Fitaccen Jihar Arewa

An Fara Diraman Bayan Zabe A LP Yayin Da Jam'iyyar Ta Dakatar Da Jiga-Jiganta 11 A Fitaccen Jihar Arewa

  • Jam'iyyar Labour, LP, a Jihar Nasarawa ta dakatar da wasu shugabannin jam'iyyar bisa zargin yiwa jam'iyyar zagon kasa a zaben da ya gabata
  • Cikin wanda aka dakatar akwai sakataren jam'iyyar, da shugabar mata da ma'aji da wasu shugabannin jam'iyyar a matakin kananan hukumomi
  • Shugaban jam'iyyar ya ce an kafa kwamitin bincike don tabbatar da zargin kuma za su dauki matakin da ya dace da zarar an kammala bincike

Nasarawa - Jam'iyyar LP reshen Jihar Nasarawa ta dakatar da shugabannin jam'iyyar 11 bisa zargin yiwa jam'iyyar zagon kasa a zaben gwamnan jihar da na yan majalisar jiha ranar 18 ga watan Maris.

Shugaban jam'iyyar Labour na jihar, Alexander Ombugu, da mataimakin sakatare, Ashime Benjamin, su ka sanar da haka a wata sanarwa da su ka futar ranar Laraba a Lafia, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: PDP Ta Janye Dakatarwa Da Ta Yi Wa Shema, Fayose, Da Wasu Kusoshinta 3 Bayan Tafiyar Ayu

Jam'iyyar Labour
Jam'iyyar LP na Nasarawa ta zargi manyan jiga-jiganta uku da wasu da yi wa jam'iyya zagon kasa. Hoto: Labour Party
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanarwar ta ce dakatarwar ta biyo bayan matakin uwar jam'iyyar ta kasa don magance faruwar haka tsakanin yan jam'iyyar a gaba.

Ta kara da cewa an dakatar da shugabannin daga duk wani sha'anin jam'iyyar a matakin jiha da karamar hukuma, rahoton The Punch.

Daga cikin wanda aka dakatar akwai sakataren jam'iyyar, Dahiru Abubakar; shugabar mata, Hajara Dalhatu; da ma'aji, Musa Doma.

Sauran sun hada da shugabannin jam'iyyar a kananan hukumomi, sun hada da karamar hukumar Keffi, Kurah Tente; karamar hukumar Obi, Ashefo Jubrin; karamar hukumar Akwanga, Promise Ezekiel; Karamar hukumar Karu, Muhammad Aruwa; karamar hukumar Nasarawa, Abdullahi Eya; karamar hukumar Awe, Abdulrahman Kasimu; karamar hukumar Nasarawa Eggon, Achuku Ibrahim; da karamar hukumar Lafia, Muhammad Aliyu.

Ombugu ya ce:

''A dalilin wata takardar korafi da aka turawa uwar jam'iyyar LP ta kasa mai dauke da kwanan wata 24/3/2023 saboda saba doka da wasu shugabannin jam'iyyar a matakin jiha da kananan hukumomi su ka yi jam'iyyar da kuma martanin da aka samu.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Za Ta Titsiye Sanata Da Wani Dan Majalisar Wakilai Daga Jihar Gombe Bisa Zargin Cin Dunduniyar Jam'iyya

''Mu na so mu sanar da ku cewa wadanda mu ka dakatar sun sabawa dokokin jam'iyyar a sashe na 19 bangare 'B' da lamba ta 2, wanda ya tanadi hukuncin da za a dauka kan wanda ya yi zagon kasa da ya janyo bacin rai da raina jam'iyya.
''A shirye-shiryen zaben gwamna, dan takarar gwamnanmu, Joseph Ewuga, ya janyewa dan takarar PDP, David Ombugadu.
''Ya sanar da jam'iyyar kuma mu ka sanar da uwar jam'iyyar ta kasa amma wasu daga cikin masu zartarwar jam'iyyar a Jihar Nasarawa sun yi gaban kansu tare da goyawa wani dan takarar daban baya ba tare da izinin LP ba; shi ya sa aka dakatar da su yau.''

Ombugu ya kara da cewa an kafa kwamitin mutum biyar tare da ba su sati biyu don gudanar da bincike akan wanda aka dakatar.

''Idan aka same su da laifi, za a dauki matakin da ya dace su bisa dokokin jam'iyya.'' in ji shi.

Kara karanta wannan

Matsala Ta Faru: Masu Ruwa da Tsaki Sun Mamaye Sakatariyar PDP a Abuja Bayan Maye Gurbin Ayu

Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya shirya hakura da takara saboda a kayar da Atiku

A wani rahoton kun ji cewa Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya ce ya shirya yafe takara don ganin Peter Obi ya zama shugaban kasa.

Ortom, wanda ke neman sanata na yankin Benue ta Arewa maso Yamma a majalisar dattijai ya ce yana iya hakura da takararsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel