Babban Abinda Ya Jawo APC Ta Sha Kaye a Zaben Gwamnan Kano, Shugaban Matasa
- Jam'iyyar APC ta samu babbar tangarɗa sakamakon rashin nasara hannun NNPP a zaben gwamnan jihar Kano
- Ahmed Abba Ɗanagata, tsohon ɗan takarar shugaban matasa, ya ce APC ta sha ƙasa ne saboda rikicin cikin gida
- Matashin ɗan siyasan ya bayyana abinda yake hangen idan APC ta yi zata iya kwato mulkin Kano daga hannun NNPP mai kayan marmari
Kano - Ɗaya daga cikin babban abun takaicin da zaben gwamnonin wannan shekarar ya zo da shi a Najeriya shi ne rashin nasarar jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kano.
Ɗan takarar gwamna karkashin inuwar NNPP mai kayan marmari, Abba Kabir Yusuf, ya lallasa takwaransa na APC kuma mataimakin gwamna, Nasir Yusuf Gawuna.
Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida ya samu kuri'u 1,019,602 yayin da Gawuna ya zo na biyu da kuri'u 890, 705.
Duba da ƙarfin kuri'un Kano wajen canja wasan, ana ganin wannan babbar rashin nasara ce ga jam'iyyar APC domin da yuwuwar ta ci gaba da kawo wa jam'iyar tangarda a zaɓuka masu zuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa APC ta sha kaye a zaɓen Kano?
Da yake hira da Legit.ng Hausa, Ahmed Abba Ɗangata, tsohon ɗan takarar shugaban matasan APC, yace rigingimun cikin gida suka haddasa rashin nasarar jam'iyyar.
Ɗangata ya ce rashin sulhunta rigimar cikin gida a APC ne ya jawo jiga-jigai kamar Kawu Sumaila, Kabiru Alasan da Sha'aban Sharaɗa suka sauya sheƙa zuwa wasu jam'iyyun.
"A jihar Kano, jam'iyya mai mulki ta gaza kaiwa ga nasara ne ba wai don rashin nagarta ko kwarewar ɗan takararta, Nasir Gawuna ba," inji shi.
Menene mafita ga APC?
Dangata ya ƙara da cewa hanya ɗaya da APC zata dawo da martabarta a Kano shi ne shugabanni su zauna su sake lale, su jawo kowane mai ruwa da tsaki, ba iya shafaffu da mai ba.
"Na Sama Da Mu Sun Karbi Tuhumar", 'Yan Sanda Sun Bayyana Halin Da Ake Ciki Game Da Shari'ar Ado Doguwa
Ya ce ya kamata gwamnatin Kano karkashin gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje, ta rika sauraro da magance ƙorafe-ƙorafen al'umma musamman matasa, ma'aikata da 'yan fansho.
A wani labarin kuma Jam'iyyar LP ta faɗi yuwuwar Sanatoci 8 da yan majalisar wakilan tarayya 34 su sauya sheka bayan rantsarwa
Shugaban LP na ƙasa ya ce zababbun mambobin majalisun tarayya da suka samu galaba a zaben da ya gabata karkashin LP ba zasu yi butulci ba.
Asali: Legit.ng