Sihiri Aka Mun Na Bar Kwankwaso Na Koma Wurin Ganduje, Ali Artwork

Sihiri Aka Mun Na Bar Kwankwaso Na Koma Wurin Ganduje, Ali Artwork

  • Fitaccen jarumin Kannywood kuma ɗan wasan barkwanci, Ali Artwork Maɗagwal, ya ce asirce shi aka yi a siyasar Kano
  • Maɗagwal kamar yadda aka fi saninsa, ya ce ya bar Kwankwasiyya ya koma tsagin Ganduje ne sabida an sihirce shi
  • Ɗan wasan barkwanci yana ta fafutukar mi'ara koma baya zuwa Kwankwasiyya amma abun ya ci tura

Kano - Jarumi kuma mai nishaɗantarwa a Kannywood, Ali Muhammed Idris Artwork, wanda aka fi sani Maɗagwal ya ce ya bar Kwankwasiya zuwa Gandujiyya saboda an masa asiri.

Daily Trust ta ce Rabiu Kwankwaso ne jagoran ɗarikar Kwankwasiyya yayin da gwamna Abdullahi Ganduje ke jagontar Gandujiyya a siyasar Kano ta dabo.

Ali Artwork da Abba Gida Gida.
Jarumi Madagwal tare da Abba Kabir Yusuf Hoto: Ali Artkwork
Asali: Facebook

Dukkan sansanonun biyu sun yi gaba da gaba da juna a zaɓen gwamna ranar 18 ga watan Maris, 2023, inda NNPP ta Kwankwaso ta tumurmusa APC karkashin Ganduje.

Kara karanta wannan

"Dama Na Faɗa" Gwamna Wike Ya Maida Martanin Kan Maye Gurbin Shugaban PDP Na Kasa

Yayin da yake martani kan kalaman da magoya bayan Kwankwasiyya ke yi a kafafen sada zumunta, Maɗagwal ya ce asirce shi aka yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan Kwankwasiyya sun bayyana cewa ba zasu karbi tubar Jarumin ba ko da kuwa ya nemi a masa wankan tsarki ya dawo inuwar Kwankwaso bayan NNPP ta ci Kano.

Sun yi ikirarin cewa Ali Artwork watau Maɗagwal ya musu kalaman rashin kunya har da taɓa Madugun Kwankwasiyya lokacin da ake tunkarar zaɓe.

A sahihin shafinsa na dandalin Facebook, Artwork ya ce ya kamata mutane su fahimci cewa ba yin kansa bane asiri aka masa sabida haka ya dace a masa uzuri.

"Asiri aka mun, shiyasa na koma ɗayan ɓangaren amma Alhamdulillah na dawo cikin hanyyaci na bayan Addu'o'i da neman magani. Tun asali ni ɗan ɗarikar Kwankwasiyya ne tun 2019."

Maɗagwal ya yi yunkurin komawa wa tafiyar Kwankwasiyya bayan INEC ta ayyana Abba Gida-Gida a matsayin wanda ya ci zaɓen Kano amma magoya baya sun tare ko ina.

Kara karanta wannan

Babbar Kotu Ta Kori Ɗan Majalisar Arewa Daga Mukaminsa Kan Muhimmin Abu 1

"Ɗama Na Faɗa Maka Sai Ka Tafi" Gwamna Wike Ya Yi Murna da Maye Gurbin Ayu

A wani labarin kuma Gwamna Wike ya bayyana farin cikinsa yayin martani kan matakin maye gurbin Ayu da PDP ta ɗauka

Gwamnan jihar Ribas yace duk makirce-makircen da aka ƙulla musu a yanzun ƙaiƙayi ya koma kan mashekiya kuma dama ya ɗauki alkawari.

Ya ce Ayu ya daina ruɗuwa da lauyoyin da ke kewaye da shi domin haka ta faru da tsohon shugaban PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262