Yan Najeriya Zasu Yi Dokin Buhari Bayan Ya Sauka Daga Mulki, Shehu

Yan Najeriya Zasu Yi Dokin Buhari Bayan Ya Sauka Daga Mulki, Shehu

  • Malam Garba Shehu, ya ce 'yan Najeriya za su yi kewar shugaba Muhammadu Buhari idan ya sauka daga mulki
  • Kakakin shugaban kasan ya ce abinda ya faru da Jonathan bayan ya sauka daga mulki, haka zata faru da Buhari bayan 29 ga watan Mayu
  • Ya ce maganar takaita hada-hada da takardun naira da gwamnatin Buhari ta zo da shi ba gudu ba ja da baya

Abuja - Babban mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yaɗa labarai, Malam Garba Shehu, ya ce 'yan Najeriya zasu kewa da ɗokin shugaba Muhammadu Buhari bayan ya bar Ofis ranar 29 ga watan Mayu.

Garba Shehu ya bayyana haka yayin wata hira da gidan Talabijin ɗin Channels a cikin shirin Sunrise Daily ranar Litinin 27 ga watan Maris, 2023.

Shugaba Muhammadu Buhari.
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari Hoto: Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Kakakin shugaban kasan ya ce sanannen abu ne 'yan Najeriya ba su kaunar shugabanninsu a lokacin da suke kan madafun iko, amma suna kewarsu bayan sun sauka.

Kara karanta wannan

Abu Ya Girma: Babbar Kotu Ta Dakatar da Shugaban PDP Na Ƙasa Nan Take Kan Muhimmin Abu 1

Garba Shehu ya koka kan yawan sukar shugaba Muhammadu Buhari, inda ya ƙara da cewa al'adar yan Najeriya ce hantarar shugabansu mai ci kafin ya bar Ofis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadimin Buharin ya ce tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, "Wanda mutane suka hukunta ta hanyar raba shi da mulki, ya zama wanda 'yan Najeriya suke kauna."

A cewarsa, abinda ya faru na ɗokin Jonathan ne zai maimaita kansa bayan shugaba Muhammadu Buhari ya miƙa mulki ga shugaban kasa na gaba.

Game da batun canjin naira kuma, Shehu ya ce sabon tsarin takaita yawan kuɗi a hannu da wannan gwamnatin ta bullo da shi abu ne mai kyau kuma ba za'a fasa ba.

Vangaurd ta rahoto Shehu na cewa:

"Takaita yawon takardun kuɗi ci gaba ne ga Najeriya saboda duk wata ƙasa da ake ganin ta ci gaba, ta jima da komawa wannan tsarin."

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye

Babbar Kotu Ta Kori Ɗan Majalisar Arewa Daga Mukaminsa Kan Muhimmin Abu 1

A wani labarin kuma Babbar Kotun tarayya mai zama a Yola ta tsige ɗan majalisar dokokin jihar Adamawa daga kan kujerarsa.

Alkalin Kotun ya yanke hukunci ne bayan gamsuwa da bayanan APC kan ɗan majalisar wanda ya sauya sheka zuwa PDP bayan ya ci zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262