Yan Sanda Sun Kama Mutane 79 da Suka Ta Da Yamutsi a Zaben Gwamnan Sakkwato
- Hukumar yan sanda reshen jihar Sakkwato ta bayyana matakin da ta ɗauka kan mutanen da ta kama lokacin zaben gwamna
- Mai magana da yawun hukumar, DSP Sanusi Abubakar, ya ce sun miƙa wa INEC wasu, sun gurfanar da wasu a Kotu
- A ranar 18 ga watan Maris, 2023 aka gudanar da zaben gwamna da mambobin majalisar dokokin jiha
Sokoto - Rundunar 'yan sandan Sakkwato ta ce jami'an tsaro sun damƙe mutane 79 da ake zargi da karya doka da oda lokacin zaben gwamna da 'yan majalisun jiha.
The Nation tattaro cewa hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan jihar, DSP Sanusi Abubakar, ya fitar ranar Lahadi.
Yace wandanda aka cafke sun kunshi mutanen da suka saɓa wa umarnin takaita zirga-zirgan ababen hawa da wasu laifuka da suka saɓa wa dokokin zaɓe.
A cewarsa, ranar zaɓe hukumomin tsaro sun gamu da Kes kala daban-daban kuma sun kame masu hannu a sayen kuri'u, fasa akwatin zabe, ta da zaune tsaye da barazanar ga zaman lafiyar al'umma da sauransu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
DSP Abubakar ya ce:
"Duk waɗanda suka aikata laifin da ya saba wa dokokin zaɓe mun gama bincike a kansu kuma mun miƙa su hannun hukumar zaɓe INEC domin ta hukunta su."
"Ragowar waɗanda suka yi wa dokokin Fenal Kod karan tsaye kuma 'yan sanda sun gurfanar da su a gaban Kotu. Har yanzun akwai sauran waɗanda suke karkashin bincike."
Kakakin yan sandan ya ce kwamishinan hukumar yan sanda ta jihar, Muhammed Gumel, ya roki ɗaukacin mutane da su guji shiga aikata duk abinda ya saɓa wa doka.
Vangaurd ta rahoto Gumel na cewa:
"Ina kira ga ɗaukacin mutane su kare kansu ko 'yan uwansu daga duk wani aiki da ya yi hannun riga da tanadin doka, musamman yayin da ake tunkarar karishen zaɓw a Sakkwato."
INEC Ta Yi Mun Daidai da Ta Ayyana Zaben Adamawa da Bai Kammalu Ba, Inji Binani
A wani labarin kuma Yar takarar gwamna mace a jihar Adamawa, Aishatu Binani, ta maida martani kan zaben gwamnan da ya gabata
Sanata Binani, ta roki INEC ta sake nazari kan sakamako a kananan hukumomi 16 daga cikin 21 da ke faɗin jihar Adamawa.
Asali: Legit.ng