Yadda Rikicin 'Yan PDP da Gwamna a Arewa Suka Jawo Fasto Ya Ci Zaben Gwamna

Yadda Rikicin 'Yan PDP da Gwamna a Arewa Suka Jawo Fasto Ya Ci Zaben Gwamna

Rabaren Hyacinth Alia ya samu karbuwa a jihar Benuwai, zai zama sabon Gwamna a watan Mayu

Ana ganin nasarar Jam’iyyar APC a zaben na 2023 ba ta rasa alaka da rikicin cikin gidan PDP

A karshe Samuel Ortom zai mika mulki ga Hyacinth Alia, a maimakon ‘dan takaran da ya ci buri

Benue - Rabaren Hyacinth Alia wanda Fada ne a coci, shi ne wanda ya yi nasara a zaben sabon Gwamna da hukumar INEC ta shirya a jihar Benuwai.

A wani rahoto na musamman, Daily Trust ta dauko labarin siyasar Hyacinth Alia ganin yadda ya doke ‘dan takaran jam’iyyar PDP a Benuwai a bana.

Faston ya yi galaba a kan Injiniya Titus Uba wanda jam’iyyar PDP ta tsaida da ratar kuri’u 251, 020.

Kara karanta wannan

Uba Sani: ‘Dan Takaran Gwamnan Kaduna Zai Kai Jam’iyyar PDP Kotu Duk da Ya Ci Zabe

Farfesa Adamu Farouk Kuta na jami’ar tarayya ta Minna ya ce APC ta samu kuri’u 473, 933 a zaben, sai PDP da LP su ka samu 223, 913 da kuma 41, 881.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Benuwai ta na da kananan hukumomi 23, Hyacinth Alia ya yi galaba a 17 daga cikinsu, ‘dan takaran PDP ya ci hudu, sai jam’iyyar LP ta samu guda.

Faston ya shahara ne a wajen warkar da mutane a wajen hudubarsa ta ranar Lahadi. Kwatsam sai aka ji ya shiga siyasa, zai nemi takarar Gwamna a APC.

APC Benue
Yakin zaben APC Hoto: www.nairaland.com
Asali: UGC

'Yan takarar Gwamnan Benuwai

Abokan takararsa a zaben 2023 sun hada da Dr. Mathias Oyigeya, Dr. Roseline Ada Chenge, Joseph Waya, Herman Hembe da shi Injiniya Titus Uba.

Sauran ‘yan takaran su ne Dr. Sam Abah, Dr. Roberts Orya, Aondona Sharon Dabo-Fiase da su ka nemi mulki a APC, ADP, APGA, LP, PDP da sauransu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: INEC Ta Bayyana Sakamakon Zaben Gwamna a Jihar Enugu Mai Cike da Ruɗani

Rahoton ya ce a cikin ‘yan takaran, babu wanda ya samu karbuwa irin Rabaren din saboda sunan da ya yi a coci da farin jini da ya yi a wajen talakawa.

Ya aka yi PDP ta sha kasa?

Masu nazari su na ganin Injiniya Uba da jam’iyyar PDP ta tsaida bai taimaka mata ba, shugaban majalisar dokokin bai da nauyi a siyasar jihar Benuwai.

Ana ganin Dr. Iyorchia Ayu da Samuel Ortom duk su na tare da Uba a farkon tafiya, amma da rikicin G5 ya yi kamari, sai barakar jam’iyyar PDP ta yi fadi.

Wadanda ke tare da shugaban PDP na kasa sun yaki Gwamna Ortom da ‘dan takaransa. A karshe wannan ya taimaka Fasto Alia wajen yin nasara.

Yayin da Alia ya rika samun karbuwa a kauyuka, jama’a da-dama su na kuka da gwamnatin PDP da ta gaza biyan fansho da albashin ma’aikatan jiha.

Za a fara rabon satifiket

Kara karanta wannan

Shekarau da Jiga-Jigan 'Yan siyasa 8 da Suka Tafka Asara 10 da 20 a Zaben Bana

An samu labari cewa zababbun Gwamnonin jihohi da Mataimakansu da aka zaba a Jihohin Najeriya za su karbi satifiket daga hannun hukumar INEC.

Sannan INEC za ta raba takardun shaidar nasara ga zababbun ‘Yan Majalisa fiye da 900. Alamu na nuna INEC ba ta da niyyar sake nazarin zaben jihohi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng