Fadar Shugaban Kasa Ta Magantu Kan Zargin Cewa Buhari Ba Zai Mika Mulki Ga Tinubu Ba Ranar 29 Ga Watan Mayu

Fadar Shugaban Kasa Ta Magantu Kan Zargin Cewa Buhari Ba Zai Mika Mulki Ga Tinubu Ba Ranar 29 Ga Watan Mayu

  • Garba Shehu ya ce shirin gwamanatin Buhari na mika mulki ga shugaban kasa mai jiran gado, Bola Tinubu, ya yi nisa
  • Mai magana da yawun shugaban kasar ya bayyana haka a wani martani kan batun da ke yawo a kafafen sadarwa cewa Buhari ba shi da niyyar mika mulki ga Tinubu
  • Shehu ya kara da cewa Buhari ya kosa ya bar fadar shugaban kasa ya kuma koma mahaifarsa a Daura, da ke jihar Katsina

Gidan Gwamnati, Abuja - Fadar shugaban kasa a ranar Juma'a, 24 ga watan Maris, ta karyata rahotannin da ke cewa Shugaba Muhammadu Buhari ba shi da niyyar mika mulki ga zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, a karshen wa'adin mulkinsa ranar 29 ga watan Mayu.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Garba Shehu ya fitar ya ce, tuni shirin gwamnati na mika mulki ya yi nisa, a cewar rahoton gidan talabijin na Channels.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Yi Alfahari, Ya Bayyana Yadda Ya Hana Siyan Kuri'a A Zaben 2023

Buhari da Tinubu.
Fadar shugaban kasa ta ce Buhari ya kagara ya mika mulki ga Tinubu ranar 29 ga watan Mayu. Hoto: Fadar Shugaban Kasa
Asali: Facebook

Wani bangaren sanarwar ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

''Fadar shugaban kasa na son sanar da cewa labarin karya ne kuma mara makama, ta kuma yi Allah wadai da jingina kalaman karya ga shugaba Muhammadu Buhari da kuma yada shi.
''Ta ya zaka tallata wani iya karfinka, ka zabe shi sannan ace ba za ka mika ma sa mulku ba? Wannan tunanin marasa ilimi ne.''

Shehu bayyana kafar yada labaran da ta wallafa rahoton (ba Legit.ng ba) a matsayin ''mara sanin ya kamata'' ya kara da cewa mammalakinta ''ya dauki bangare a siyasa, hasalima ya fadi a zaben shugaban kasa.''

Daga Buhari zuwa Tinubu: Fadar Shugaban kasa ta yi bayanin shirin mika mulki

Shehu kuma cigaba da cewa a kafa kwamitin mika mulki, da ya hadar da wakilan gwamnatin Buhari da kuma gwamnati mai jiran gado ta Tinubu.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Ba Zan Taba Zama Dan APC Ba, Inji Fayose

A cewarsa, kwamitin na tattaunawa kullum.

''Tuni gwamnati ta fara shirin mika mulki. Kwamitin mika mulki, da ya hadar da wakilan gwamnati mai barin gado da mai jiran gado su na tattaunawa kusan kullum don shirya yadda za a mika mulki ga gwamnatin Tinubu/Shettima,'' in ji shi.
''Akwai kananan kwamitoci 13 da aka fitar daga babban kwamitin, wasu, don shirya faretin sojoji da kuma raka shugaba Buhari, sun fara aikinsu ko su na daf da farawa. Zuwa yanzu, komai na tafiya dai dai kuma ba alamun tangarda.''

Buhari ya matsu ya koma Daura, in ji Shehu

Shehu ya kuma bayyana cewa shugaban kasar ya kosa ya koma garinsu Daura, da ke Jihar Katsina, don more hutun barinsa aiki.

Ya ce al'ummar Daura sun fara shirye shiryen tarbar dan su bayan ''kammala mulkinsa cikin nasara har na wa'adi biyu tsahon shekara takwas.''

Na kagu in bar aiki, cewar Buhari

Kara karanta wannan

Na Ƙagu In Tafi, In Ji Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

A wani rahoton, shugaba Buhari ya ce ya matsu ya bar kujerar shugaban kasa kamar yadda aka tanada ranar Litinin, 29 ga watan Mayu.

Da ya ke zantawa da jakadiyar Amurka mai barin gado, Mary Beth Leonard, shugaban ya bayyana cewa ya na fatan zama ''babban manomi'' a garin su Daura da ke Jihar Katsina.

Shugaba Buhari ya kuma ce da zarar ya bar ofis, zai koma aiki a gonarsa tare da kula da dabbobinsa sama da 300 a garinsu, Daura da ke Jihar Katsina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164