Jam'iyyar PDP Ta Dakatar da Shema, Fayose da Wasu Jiga-Jiganta Na Kasa
- Jam'iyyar PDP ta kasa ta dakatar da manyan jiga-jiganta guda 5 bisa zargin zagon ƙasa da cin amana
- Daga cikin waɗanda matakin ya hau kansu har da tsohon gwamnan Katsina, Ibramin Shema da tsohon geamnan Ekiti, Ayodele Fayose
- Bayan haka jam'iyyar ta miƙa makomar gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom ga kwamitin ladabtarwa
Abuja - Jam'iyyar PDP ta ƙasa ta dakatar da tsohon gwamnan jigar Katsina, Ibrahim Shema, Tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose da wasu manyan jiga-jigai.
A wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Tuwita, PDP tace ta dakatar da ƙusoshinta 5 ne saboda zarginsu da cin amana da yi wa jam'iyyar zagon ƙasa.
Baya ga haka, PDP ta miƙa gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ga kwamitin ladabtarwa bayan ta samu rahoton yana shiga wasu harkokin cin amanarta.
Gwamna Matwalle Ya Karbi Kaddara, Ya Amince Da Kayen Da Ya Sha, Ya Nemi Wata Alfarma Wajen Al'ummar Zamfara
Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Sakataren watsa labarai na jam'iyyar PDP ta ƙasa, Honorabul Debo Ologunagba, ya fitar ranar Alhamis, 23 ga watan Maris, 2023.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sanarwan ta ce:
"Kwamitin gudanarwa na PDP (NWC), bayan nazari kan harkokin jam'iyya a kasa duba da kwansutocin ɗin PDP ya miƙa gwamnan Benuwai Samuel Ortom ga kwamitin ladabtarwa kan zargin cin amana."
"Haka nan NWC ya amince da ɗaukar matakin dakatarwa kan waɗan nan mutanen da zasu biyo baya daga PDP kuma zai fara aiki yau Alhamis, 23 ga watan Maris, 2023."
1. Ayodele Fayose (Jihar Ekiti)
2. Ibrahim Shema (Jihar Katsina)
3. Sanata Pius Anyim (Jihar Ebonyi)
4. Farfesa Dennis Ityavyar (Jihar Benuwai)
5. Dakta Aslam Aliyu (Jihar Zamfara)
Bayan haka, jam'iyyar PDP ta bukaci shugabanni, masu ruwa da tsaki da baki ɗaya mambobin jam'iyya da ke faɗin kasar nan su ci gaba da zama kai a haɗe kuma su jure wa wannan lokacin.
Mata sun yi zanga-zanga a Kaduna
A wani labarin kuma Daruruwan Mata Sun Fito Zanga-Zangar Adawa da Nasarar Sabon Gwamnan Kaduna
Wasu dandazon mata magoya bayan jam'iyyar PDP sun gudanar da zanga-zanga a Sakatariyar NUJ domin nuna fushinsu da sakamakon zaben gwamnan Kaduna.
Shugabannin tawagar masu zanga-zangar sun nemi INEC ta ayyana Isah Ashiru Kudan a matsayin halastaccen wanda ya ci zaɓe.
Asali: Legit.ng