"Na Shirya Tsaf Domin Sauke Nauyin Da Kuka Doramin", Zababben Gwamnan Abia
- Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Abia a ƙarkashin inuwar jam'iyyar Labour Party (LP), Alex Otti, ya miƙa godiyar sa ga al'ummar jihar
- Alex Otti ya kuma basu tabbacin cewa a shirye yake da ya aiki tuƙuru wajen ganin ya sauke nauyin da suka ɗora masa
- Zaɓaɓɓen gwamnan shine na farko da jam'iyyar LP ta samu a zaɓen gwamnonin da aka yi a ƙasar nan
Jihar Abia- Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya nuna ɗumbin godiyar sa ga mutanen jihar bisa gudunmawar da suka bashi a lokacin zaɓe. Rahoton The Cable
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) a ranar Laraba ta sanar da Alex Otti, a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar, bayan ta dawo cigaba da tattara sakamakon zaɓen.
Sa'o'i kaɗan bayan an bayyana shi a matsayin zaɓaɓɓen gwamna, Otti ya bayyana cewa sabon haƙƙin da ya rataya a wuyan sa yanzu shine yayi al'ummar jihar Abia hidima.
Wata Sabuwa: Magoyan APC Sun Dira Ofishin INEC, Suna Zanga-Zanga Kan Kayen Da Dan Takarar Gwamnan Su Ya Sha
Zaɓaɓɓen gwamnan ya rubuta a shafin sa na Twitter cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Cike da ƙanƙan da kai da sanin girman alhakin dake a kai na, na amince na da zuciya da ɗaya na zaman babban hadimin ku na shekara huɗu masu zuwa nan gaba."
An samu tarnaƙi wajen tattara sakamakon zaɓen
A ranar Litinin hukumar INEC ta dakatar da tattara sakamakon zaɓe a Abia bayan ƴan daba sun farmaki ofishin ta a ƙaramar hukumar Obingwa.
Maharan sun tsare jami'an hukumar ta INEC kafin daga baya suka sake su, wanda hakan ne ya sanya hukumar yin dogon nazari kan zaɓen.
A lokacin da aka dakatar da tattara sakamakon zaɓen, Otti yana a kan gaba bayan ya samu ƙuri'u 80,000.
Bayan an tattara sakamakon zaɓen ƙaramar hukumar Obingwa, Otti ya samu ƙuri'u 175,467, inda yayi kan abokin hamayyar sa Okey Ahiwe, na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), wanda ya samu ƙuri'u 88,529.
Nasarar Alex Otti itace ta farko da jam'iyyar Labour Party (LP) ta samu zaɓen gwamnoni na ranar 18 ga watan Maris 2023.
APC ta Dakatar da SGF, Jam’iyya na Binciken Sanata, An Jero Zargin da Ake Yi Masu
A wani labarin na daban kuma, jam'iyyar APC ta dakatar da sakataren gwamnatin tarayya.
Jam'iyyar za ta kuma bincika sanatan ta bisa zargin aikata wasu laifuka a lokacin zaɓe.
Asali: Legit.ng