2023: Jam'iyyar PDP Ta Samu Galaba a Zaben Gwamnan Jihar Enugu
- Hukumar zabe INEC ta kawo karshen rudani, ta bayyana sakamakon zaben gwamna a jihar Enugu
- Baturen zaɓe ya ayyana ɗan takarar PDP a matsayin wanda ya samu nasara kuma ya zama gwamna mai jiran gado
- A dazu da safe, INEC ta ƙarisa tare da bayyana wanda ya kai ga nasara a zaben gwamnan Enugu
Enugu - Hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta ayyana ɗan takara a inuwar Peoples Democratic Party (PDP), Peter Mbah, a matsayin wanda ya samu nasara a zaben gwamna a jihar Enugu.
Daily Trust ta rahoto cewa sakamakon zaben da INEC ta bayyana da daren Laraban nan, ya nuna cewa Mista Mbah, ya samu kuri'u 160,895.
Hakan ya ba shi damar lallasa babban abokin karawarsa na jam'iyyar Labour Party (LP), Chijioke Edeoga, wanda ya samu kuri'u 157,552.
Uche Nnaji na jam'iyyar All Origressive Congress (APC) ya samu kuri'u 14,575, kamar yadda The Cable ta rahoto.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Da yake sanar da sakamakon zaben, baturen zaɓe mai alhakin tattara sakamakon jihar Enugu kuma shugabar jami'ar koyon aikin gona Michael Okpara, Farfesa Maduebibisi Ofo-Iwe, ya ce:
"Mbah Peter Ndubuisi na jam'iyyar PDP, bayan cika sharuddan da doka ta tanada na ayyana shi a matsayin wanda ya samu nasara kuma ya zama zaɓaɓɓe."
Tun da fari, INEC ta kasa ta dakatar da tattara sakamakon zaben gwamnan Enugu mai cike da ruɗani kana ta kira manyan jami'anta na jihar suka tafi birnin tarayya Abuja.
A safiyar Laraba 22 ga watan Maris, 2023, hukumar zaben ta sanar da cewa nan da 'yan awanni zata bayyana sakamakon zaben gwamnan da aka gama ranar Asabar.
Legit.ng Huasa ta fahimci cewa a jihar da ke maƙotaka da ita a kudu maso gabas watau Abiya, INEC ta ayyana, Alex Otti, na LP a matsayin gwamna mai jiran gado.
A halin yanzun jihohin Adamawa da Kebbi ne kaɗai suka rage ba'a bayyana wanda ya samu nasara ba daga cikin jihohi 28 da aka gudanar da zaɓe ranar Asabar.
DSS ta kama ɗan majalisar jiha a Enugu
A wani labarin kuma DSS Ta Damƙe Ɗan Majalisa Kan Hannu a Laifin da Ya Shafi Karancin Naira
Jami'an tsaro DSS sun cafke ɗan majalisar jiha na jam'iyyar PDP bisa zarginsa da hannu a tashin-tashinar da ya biyo bayan zanga-zanga kan karancin takardun naira.
Asali: Legit.ng