Dadi Kamar Ya Kashe Matar Gwamna, Mata 6 Sun Samu Kujera a Majalisa a Zaben 2023
- Mai dakin Gwamnan Ekiti, Olayemi Oyebanji ta ji dadin ganin sakamakon zaben ‘Yan majalisa
- Uwargidar jihar tayi farin ciki ne da yadda mata shida da suka nemi kujerar majalisa suka yi nasara
- Bose Olowookere, Bolaji Olagbaju, Abimbola Solanke da wasu mata 3 za su je majalisa a 2023
Ekiti - A ranar Litinin ne Uwargidar jihar Ekiti, Olayemi Oyebanji ta yi farin ciki da matan da suka lashe zaben majalisar dokoki da aka shirya.
Premium Times ta rahoto cewa Olayemi Oyebanji ta ji dadin ganin yadda mata har shida su ka zama zababbun ‘yan majalisar dokoki na Jiha.
Mai dakin Gwamna na Ekiti tayi kira ga mutane da su cigaba da ba Gwamnatin Biodun Oyebanji goyon baya da kyau domin a dama da mata.
A cikin mutane 26 da za su je majalisar dokokin Ekiti a Yunin 2023, an samu shida da mata ne. Wannan abin ayi murna ne a irin siyasar Najeriya.
Jihar Ekiti ta zama abin kwatance
An rahoto Oyebanji tana cewa Ekiti ta zama abin koyi a cikin Jihohin Najeriya domin za ta zama inda ta fi kowcae yawan mata a majalisar jiha.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit.ng Hausa ta fahimci a wasu da-dama daga jihohin Arewacin kasar nan, babu mace ko daya da ta ke wakiltar mazabarta a majalisar dokoki.
Shugabar majalisar Jihar Ekiti, Rt. Hon. Olubunmi Adelugba ta ji dadin yadda aka samu karin mata a sakamakon zaben 2023 da aka gudanar.
Vanguard ta rahoto Olubunmi Adelugba tana cewa hakan alamar cewa mata su na cigaba ne a kasar.
"Ina farin ciki domin matan da ke majalisa ba su ragu ba, sai dai ma karuwa suke yi.
Ina yawan faawa abokan aiki na da za su dawo, majalisa ta bakwai za tayi kyau, musamman da aka samu karin mata, idan mata suka yi kyau, wuri ya gyaru."
Mata 6 da suka ci zabe a APC
Jaridar ta ce matan da za a gani idan an rantsar da majalisa nan a ‘yan watanni su ne: Bose Olowookere (Efon) da Iyabo Fakunle-Okiemeh (Ilejemeje).
Sannan akwai Mariam Ogunlade (Emure), Bolaji Olagbaju (Ado II), Teju Okuyiga (Gbonyin), sai Abimbola Solanke (Moba) da za su wakikci mutanensu.
Asali: Legit.ng