Jam'iyyar PDP Ta Lashe Zaben Gwamna a Jihohin Delta da Filato
- Jam'iyyar PDP ta samu nasarar kwace mulki a jihar Filato da ke arewa ta tsakiya a Najeriya, ɗan takararta ya zama gwamna mai jiran gado
- Haka nan a jihar Delta, abokin takarar Atiku Abubakar, gwamna Ifeanyi Okowa ya samu nasarar kawo wa jam'iyyarsa nasara
- INEC na ci gaba da tattara sakamkon zaben gwamnoni wanda ya gudana ranar 18 ga watan Maris, 2023 a jihohi 28
Jam'iyyar PDP ta samu nasarar lashe zaben gwamnonin da ya gudana ranar Asabar 18 ga watan Maris, 2023 a jihohin Delta da kuma Filato.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa yayin da PDP ta samu nasarar ci gaba da mulki a jihar Delta, a jihar Filato ta tumurmusa APC ta kwace mulki daga hannunta.
Yadda sakamakon zaɓen gwamna a jihohin ya nuna
A jihar Filato, ɗan takarar gwamna a inuwar PDP, Caleb Mutfwang, ya samu kuri'u 525,299 wanda suka ba shi damar lallasa babban abokin karawarsa na APC mai mulki, Nentawe Yilwatda, mai kuri'u 481,370.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Haka zalika a jihar Delta, kakakin majalisar dokokin jihar kuma ɗan takarar gwamnan PDP, Honorabul Sheriff Oborevwori, ya samu nasara da kuri'u 360,234.
Babban abokin hamayyarsa na jam'iyyar APC, Sanata Ovie Omo-Agege, ya tashi da kuri'u 240,229, yayin da takawaransu na Labour Party, Ken Pella, ya zo na uku da ƙuri'u 48,047.
Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa har yanzun akwai jihohin da hukumar INEC ba ta kammala tattara sakmakon zaben gwamna ba kamar Borno, Adamawa, Abia, Enugu, Ribas da sauran su.
A jihar Adamawa da jam'iyyar PDP ke mulki ana dakon sanar da sakamako a hukumance daga bakin baturen zabe bayan bayyana alkaluman karamar hukumar ƙarshe.
INEC Ta Bayyana Sakamakon Zaben Gwamnan Bauchi
A wani labarin kuma Gwamna Bala Muhammed ya samu nasara sake koma wa kujerarsa karo na biyu a jihar Bauchi
Gwamnan, ɗan takara a inuwar PDP ya lallasa babban abokin hamayyarsa na APC, Air Marshal Saddique Abubakar, tsohon shugaban rundunar sojin sama.
Kauran Bauchi ya samu nasara a kananan hukumomi 15 cikin 20 da ke faɗin jihar Abuchi, yayin da Air Marshal ya lashe guda 5.
Asali: Legit.ng