Zaben Gwamnoni: Mun Shirya Kashe Duk Wanda Ya Shirya Mutuwa a Yau – Yan Sanda

Zaben Gwamnoni: Mun Shirya Kashe Duk Wanda Ya Shirya Mutuwa a Yau – Yan Sanda

  • A yau Asabar, 18 ga watan Maris ne za a gudanar da zabukan gwamnoni da na yan majalisar jihohi a Najeriya
  • Rundunar yan sandan kasar ta yi gagarumin gargadi ga masu shirin kawo hargitsi a shirin zaben
  • Yan sandan ta ce duk wanda yake so mahaifiyarsa ta haifi wani ba shi ba toh ya fito da sunan sace akwatunan zabe da sauransu

Abia - Rundunar yan sandan kasar ta yi gagarumin gargadi ga mutane ko kungiyoyi masu niyan kawo hargitsi a zaben gwamnoni da yan majalisar jihohi da za a yi a fadin jihohi 28 na Najeriya.

Mataimakin Sufeto Janar na yan sanda da ke da alhakin kula da yankin kudu maso gabas, John Amadi, shine ya yi gargadin a ranar Alhamis, a Umuahia, yayin da yake jawabi ga jami'an yan sandan jihar, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

2023: Jonathan Ya Ba Wa Yan Siyasa Shawara Mai Ratsa Jiki Ana Daf Da Zaben Gwamnoni

Jami'an yan sanda rike da bindiga
Zaben Gwamnoni: Mun Shirya Kashe Duk Wanda Ya Shirya Mutuwa a Yau – Yan Sanda Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ahmadi ya ce:

"Duk wanda yake son tarwatsa tsarin toh ya shirya mutuwa, duk wanda yake so ya mutu toh ya fito sannan ya tarwatsa shirin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Idan kana son ranka, ka yi nisa, ka kada kuri'arka, ga tafi gida sannan ka jira sakamako."

Za mu ba rayuka da dukiyoyin jama'a kariya, yan sanda

Mista Amadi ya yi kira ga masu zabe a jihar Abia da su yi watsi da duk wani barazana na yunkurin hana su zabe, yana mai basu tabbacin cewa za a gudanar da zaben kamar yadda aka tsara, rahoton Peoples Gazette.

"A madadin Sufeto Janar na yan sanda da tawagar gudanarwa, ina mai baku tabbacin cewa ba za a samu kowani hargitsi ba. Ina mai tabbatar maku cewa mun shirya.
"Mu na yan Najeriya ne, kuma wannan shine lokacin da za mu bari kowa ya san cewa babban aikinmu shine kare rayuka da dukiya. Mun ba yan Najeriya da kudu maso gabas tabbacin cewa kada wanda ya ji tsoro."

Kara karanta wannan

Zaben Gwamna: Rundunar Yan Sanda Ta Yi Gagarumin Gargadi Ga Al’ummar Jihar Kano Ana Gab Da Zabe

Mista Amadi ya ci gaba da cewa yan sanda na nan don kare tsarin kuma duk wanda ke son jefa kansa a matsala ko yin daba toh ya kuka da kansa.

Ya kara da cewar:

"Duk wanda ke son sace akwatunan zabe ko tarwatsa zaben zai dandana kudarsa. Mun zuba jami'anmu a dukkan yankunan da muke ganin za a samu rikici a wajen. Don haka muna yin gargadi ga miyagu da wakilan da ba na jiha ba cewa ba za mu lamunci kowani abu da zai iya hana mutane kada kuri'a ga zabinsu wanda suke so ya wakilce su ba."
Ya kuma ba baki a jihar da jami'an zabe tabbacin samun kariya, yana mai cewa: "muna kuma ba ku tabbacin cewa jami'an INEC da kayan zabe za su samu isasshen tsaro."

Rundunar Yan sanda ta gargadi al'ummar Kano

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa rundunar yan sanda ta gargadi al'ummar jihar Kano da su guji karya doka da oda yayin zaben gwamna a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng