Kai Tsaye: Yadda Zaben Gwamna Ke Gudana a Jihohin Borno, Kebbi, Zamfara da Yobe

Kai Tsaye: Yadda Zaben Gwamna Ke Gudana a Jihohin Borno, Kebbi, Zamfara da Yobe

Rana bata karya!

A Borno, Muhammad Ali Jajeri na PDP na shirin kwace kujerar gwamna Babagana Zulum na APC.

A Yobe, Gwamna Mai Mala Buni na son zarcewa kan kujerarsa amma Sharif Abdullahi na PDP na kokarin hanashi.

A Zamfara, gwamna Matawalle na takara a APC yayinda Lawal Dauda ya son kwace kujerar.

A Kebbi kuwa sabon zabe za'a yi, tsohon Soja Aminu Bande na PDP zai fafata da Nasiru Idris jam'iyyar APC

A gaban jami'an tsaro, ana sayen kuri'u a Yobe

A bainar idon jami'an tsaro, ana sayen kuri'u a Hausari Sabon Feggi, karamar hukumar Nguru. a jihar Yobe

Sanata Kashim Shettima ya kada kuri'arsa.

Mataimakin Zababben Shugaban Kasa Sanata Kashim Shettima ya kada kuri'arsa.

Shettima
Kai Tsaye: Yadda Zaben Gwamna Ke Gudana a Jihohin Borno, Kebbi, Zamfara da Yobe
Asali: Twitter

Gwamna Mai Mala Buni Ya kada kuri'arsa

Gwamnan jihar Yobe mai neman zarcewa, Mai Mala Buni, ya kada kuri'arsa a zaben dake gudana yau.

ChannelsTV ta ruwaito cewa Buni ya kada kuri'arsa a Bulturam Yerimaram a karamar hukumar Gujba.

Mataimakin gwamnan Borno ya kada kuri'arsa

TheCable ta ruwaito cewa mataimakin gwamnan jihar Borno, Kadafur, ya kada kuri'arsa a mazabarsa dake karamar hukumar ta jihar

kadafur
Kai Tsaye: Yadda Zaben Gwamna Ke Gudana a Jihohin Borno, Kebbi, Zamfara da Yobe
Asali: Twitter

Ana sayen kuri'u a Kebbi

A rumfar zaben Dan Shafarma, Koikani, karamar hukumar Argungun an ga masu sayen kuri'u kuma wakilan jam'iyyu sai sun ga abinda kowa ya zaba.

Zabe na gudana lafiya lau a Yobe

Zabe na gudana lami-lamiya a karamar hukumar Potiskum na jihar Yobe.

Kawo yanzu babu wani rahoton rikici da tashin-tashina a jihar gaba daya.

Na'uarar BVAS ta samu matsala a Kebbi

A rumfar zabe na PU 001 dake Garka Hakimi, Saransosa, karamar hukumar Maiyama dake jihar Kebbi na'urar BVAS bau daukar hotuna da ayar hannun masu zabe.

Ana jiran jama'a su zo su kada kuri'a a Yobe

Dubunnan yan gudun Hijra a Borno sun tafi kada kuri'unsu

HumAngle ta ruwaito da daruruwan yan gudun hijra suka tafi garuruwansu domin kada kuri'unsu.

Birnin Kebbi

Jami'an INEC sun dira gundumar Nasarawa, birnin Kebbi, komai na tafya dai-dai amma masu kada kuri'a basu iso ba.

Online view pixel