Tashin Hankali Yayin Da Aka Sace Dan Takarar Mataimakin Gwamna Awanni Kafin Zabe A Babban Jihar APC

Tashin Hankali Yayin Da Aka Sace Dan Takarar Mataimakin Gwamna Awanni Kafin Zabe A Babban Jihar APC

  • An yi garkuwa da dan takarar mataimakin gwamna a jam'iyyar Young Progressives Party, YPP, Prince Agbor Onyi sa'o'i kadan kafin fara kada kuri'a
  • An yi garkuwa da shi a yankin Akparavuni da ke karamar hukumar Biase da daren Alhamis tare da neman kudin fansa mai yawa
  • Jam'iyyar YPP ta bayyana cewa abin bakin ciki ne dauke dan takarar a daidai wannan lokacin, tare da yin kira ga jami'an tsaro da a gaggauta ceto shi

Cross Rivers - A shirye shiryen zaben gwamna na gobe, an yi garkuwa dan takarar mataimakin gwamna na jam'iyyar Young Progressives Party, YPP, a Jihar Cross River, Prince Agbor Onyi.

A cewar Tribune, an yi garkuwa da shi da yammacin Alhamis a unguwar Akparavuni da ke karamar hukumar Biase, kamar yadda jam'iyyar ta bayyana a sanarwar da ta fitar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Kama Mataimakin Shugaban APC Na Jiha Kwana 2 Gabanin Zabe

Jam'iyyar YPP
An sace dan takarar mataimakin gwamnan jam'iyyar YPP a Cross Rivers ana gobe zabe. Hoto: YPP
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yankin Akparavuni na karamar hukumar Biase da karamar hukumar Akamkpa da ke kan babban titin gwamnatin tarayya sun yi kaurin suna wajen garkuwa da mutane tun a shekarar da ta gabata.

Majiya ta ce maharan sun nemi kudin fansa mai yawa

Wata majiya daga iyalansa, ta ce ma su garkuwar sun bukaci kudin fansa mai yawa.

Ana ruwaito cewa an biya kudin fansar kwamishiniyar al'amuran mata, Farfesa Gerttude Njar, kuma an sakota bayan shafe sama wata a hannun ma su garkuwar.

An yi kira ga jami'an tsaro su ceto Onyi

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren jam'iyyar, Kwamared Fredrick Omari, ya ce garkuwar ta jefa iyalan Onyi mummunan yanayi.

Kalamansa:

''Mun samu labari mai ban tsoro da takaici na garkuwa da dan takarar mataimakin gwamnanmu, Prince Agbor Onyi.

Kara karanta wannan

Jerin 'Yan Takarar Gwamna 3 da Aka Raina Kuma Zasu Iya Ba Da Mamaki a Zaben Gwamnoni

''Yin wannan babban laifi a wannan gabar abin takaici ga jam'iyya kuma abin damuwa ga dukkanin mu."

Saboda haka mu na kira ga jami'an yan sanda da duk jami'an tsaro da su dauki matakin ba tare da bata lokaci ba.

''Mu na bukatar a sako dan takarar mataimakin gwamnanmu daga hannun yan garkuwa da gaggawa don ba shi damar zuwa yankin da kuma sauke nauyin sa a gobe.''

Goodluck Jonathan ya bawa yan siyasa shawara gabanin zaben gwamnoni

A wani rahoton, tsohon shugaban kasar Najeriya, Dakta Goodluck Jonathan ya shawarci yan siyasa su dena yin siyasar a-mutu ko-ayi-rai, ya kara da cewa bai kamata su kashe wadanda suke son su mulka ba.

Jonathan ya bada wannan shawarar ne a jihar Bayelsa a Sampou yayinda ya tafi ta'aziyyar rasuwar mahaifiyin Douye Diri, gwamnan Bayelsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164