An Kai Farmaki Kan Tawagar Dan Takarar Gwamnan PDP a Jihar Zamfara
- An kai farmaki kan ɗan takarar gwamnan jihar Zamfara ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Dauda Lawal
- Jam'iyyar PDP a jihar tayi zargin cewa ana ƙoƙarin ɗaukar ran ɗan takarar gwamnan nata kafin zaɓe
- Ta bayyana cewa harin na baya-bayan nan shine karo na biyu da aka kai wa ɗan takarar gwamnan a jihar
Jihar Zamfara- Jami'an kwamitin masu yaƙi da ƴan daba a jihar Zamfara sun farmaki ɗan takarar gwamnan jihar a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Dauda Lawal.
An dai farmaki tawagar motocin ɗan takarar ne a kan titin Sani Abacha na GRA a cikin ƙaramar hukumar Gusau ta jihar. Rahoton Thisday.
A wata sanarwa da ofishin watsa labarai na kamfen ɗin dan takarar ya fitar a ranar Alhamis, a Gusau, yayi zargin cewa da gangan aka kai harin kuma wani yunƙuri ne na halaka ɗan takarar gwamnan jam'iyyar PDP a jihar, Dauda Lawal.
Maso yaƙi da ƴan dabar dai sun yiwa tawagar motocin kwanton ɓauna ne sannan suka buɗe musu wuta a harin wanda ya auku a daren ranar Alhamis, inda wani ɗan sanda ya samu rauni. Rahoton Vanguard
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wannan dai shine karo na biyu a cewar ofishin watsa labaran kamfen ɗin ɗan takarar, da masu yaƙi da ƴan dabar suka yi yunƙurin halaka ɗan takarar gwamnan na jam'iyyar PDP.
Sanarwar na cewa:
"Jami'an haramtaccen kwamitin yaƙi da ƴan daba ɗauke da makamai sun farmaki tawagar motocin ɗan takarar gwamnan jam'iyyar PDP, Dauda Lawal, a ranar Alhamis 16 ga watan Maris 2023.
"Dauda Lawal yaje wasu yankuna ne domin kammala yaƙin neman zaɓen sa, sannan akan hanyar sa ta komawa gida jami'an masu yaƙi da ƴan dabar suka kai masa hari inda suka buɗewa motar sa da sauran motocin dake take masa baya wuta."
“Wannan shine karo na biyu a cikin wata da suka yi ƙoƙarin ɗaukar rayuwar ɗan takarar gwamnan jam'iyyar PDP."
“A ranar 23 ga watan Fabrairu 2023, kwamitin yaƙi da ƴan dabar ya buɗewa tawagar motocin ɗan takarar wuta wacce ke ɗauke da matar sa a ciki."
An Kashe Mutum 4 Yayin Arangama Tsakanin Yan Shi'a Da Tawagar El-Rufai A Kaduna
A wani labarin na daban kuma, an samu asarar rayuka a yayin wata taho mu gama tsakanin ƴan Shi'a da tawagar gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
Ana zargin cewa aƙalla rayuka huɗu suka salwanta a wajen.
Asali: Legit.ng