Jagora a APC Ya Ba Buhari Sunayen Wasu Mutum 2 da Zai Sallama Daga Gwamnatinsa

Jagora a APC Ya Ba Buhari Sunayen Wasu Mutum 2 da Zai Sallama Daga Gwamnatinsa

  • Prince John Mayaki yana ganin abubuwa biyu Muhammadu Buhari zai yi domin ya wanke kan shi
  • Jigon na Jam’iyya mai mulki ya yi tir da yadda aka bijirewa kotun koli kan shari’ar canjin kudi
  • Mayaki ya nemi Shugaban kasa ya sallami Gwamnan CBN da AGF domin ya nuna babu ruwansa

Edo - Prince John Mayaki jagoran jam’iyyar APC ne a jihar Edo da ke kudu maso kudancin Najeriya, ya soki Shugaba Muhammadu Buhari.

A ranar Alhamis, Tribune ta rahoto Prince John Mayaki yana cewa tofa albarkacin bakinsa ga hukuncin da kotun koli ta zartar a kan canjin kudi.

‘Dan siyasar bai gamsu da jawabin Mai girma Muhammadu Buhari da yake nesanta kansa da kunnen kashin da bankin CBN ya yi wa kotun koli ba.

Kara karanta wannan

Toh fa: Buhari ya ce yana son Tinubu ya ci gaba da yiwa 'yan kasa abu 1 da yake yi

Prince Mayaki yana ganin akwai wadanda ya dace a sallama a gwamnatin tarayya a dalilin bijirewa hukuncin Alkalan mafi girman kotun kasa.

Jigon ya shaidawa manema labarai a Abuja cewa hakan kurum shugaban Najeriyan zai yi domin nunawa ‘Yan kasa cewa bai san an sabawa kotu ba.

Shugaban kasa
Shugaban kasa a ofis Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jawabin Prince John Mayaki

"Domin ya wanke kan shi kuma ya nuna bai da hannu wajen sharrin da aka kitsawa marasa karfin ‘dan Najeriya da kananan ‘yan kasuwa, dole ya yi amfani da karfinsa a tsarin mulki da nauyin shugabancin da yake kansa, ya hukunta wadanda suka yi wannan zagon kasa.
Ba tare da kame-kame ba, bukatar mu a matsayin ‘Yan Najriya shi ne dole a hukunta wadanda suka jawo annobar da aka shiga a ‘yan watannin nan.
Kuma dole a fara da mutanen da suke kan gaba; Godwin Emefiele da babban wanda ya daure masa gindi, Ministan shari’a, Malami Abubakar SAN.

Kara karanta wannan

Canjin kudi, Kanu, ASUU da Abubuwa 5 da Tinubu Zai Ci Karo da Su da Ya Shiga Aso Rock

Wajibi ne shugaban kasa ya dauki mataki fiye da na fatar-baki domin ya dawo ya karfafawa bangaren shari’a da tattalin arzikinmu da ya rugurguje.

Ganin Godwin Emefiele ya maida kan shi ‘dan siyasa, Mayaki ya ce gwamnan CBN ya jefa tattalin arikin Najeriya cikin matsala, ya kashe kasuwanci.

Leadership ta ce zargin da ke kan Malami shi ne ya rika yi wa doka fassarar son-kai saboda siyasa, a dalilin haka ya bukaci ayi waje da shi da Emefiele.

Omisore v Lukman

A wani rahoton na dabam, an ji Mataimakin Shugaban APC ya ce Sakataren jam’iyya na kasa ya lakume kudin yin kamfen zaben shugaban kasa a jiharsa.

Bayan wannan zargi, an ji Sanata Iyiola Omisore yana neman N500m saboda zargin an bata masa suna, yana neman Salihu Lukman ya janye kalamansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng