"Ban Janye Wa Kowa Ba", Dan Takarar Gwamna Na Jam'iyyar Labour A Kaduna
- Dan takarar gwamnan Kaduna a jam'iyyar LP, Jonathan Asake, ya ce bai janye takara ba, kuma ba shi da shirin yin hakan
- Asake ya ce jita jita jam'iyyar PDP ta yada akan shi saboda tun da ya fita gwiwar jam'iyyar ta yi sanyi a jihar
- Asake ya bayyana cewa burinsa shi ne ya lashe zaben gwamnan ya kuma cika alkawarin da ya daukarwa Jihar Kaduna
Jihar Kaduna - Dan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar LP a Jihar Kaduna, Jonathan Asake, ya ce har yanzu ya na zawarcin fadar gidan gwamnatin Sir Kashim Ibrahim kuma bai janyewa kowa takara ba
Asake, ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Kafanchan, hedikwatar karamar hukumar Jema'a a jihar lokacin da ya ke mayar da martani bisa wani bayani da jam'iyyar PDP su ka fitar dangane da shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya yi jawabi ga manema labarai game da zargin kudin da Wike ya bayar don tallafawa marasa galihu a kudancin jihar, rahoton Daily Trust.
Ya ce:
''Ina samun tikitin takarar gwamna a karkashin inuwar jam'iyyar LP a watan Yulin 2022, gwiwar jam'iyyar PDP a Jihar Kaduna ta yi sanyi.''
Shugaban PDP na Kaduna ya zarge ni da cinye N120m da Wike ya bada tallafi, Asake
Ya ce shugaban jam'iyyar PDP na jihar, Hassan Hyet ya zarge shi da cinye naira miliyan 120 da Gwamna Nyesom Wike na Jihar Rivers ya tallafawa yan gudun hijira a kudancin Kaduna ta hannun kungiyar gamayyar al'umma mazauna kudancin Kaduna (SOKAPU) lokacin da ya ke shugaban kungiyar.
A cewarsa:
''Lokacin da babban kwamitin SOKAPU su ka mika rahotona ga uwar kungiya ta kasa, rahoton ya bayyana mun sayi kayan tallafi na rage radadi na kusan miiyan N60. Na kuma bar N60,954,000, wanda aka watsa sosai a kafafen yada labarai. Yayin da na ke cigaba da yakin neman zabe, zarge zarge sun cigaba bullowa musamman daga jam'iyyar PDP''.
Ba Uba Sani ke daukan nauyi na ba, Asake
Asake ya kuma karyata jita jitar cewa Uba Sani, na jam'iyyar APC ne ya dauke nauyin takararsa, da kudi miliyan N100 don ya kacaccala kuri'un kuduncin Kaduna saboda tikitin Muslim-Muslim na jam'iyyar APC ya samu nasara.
Ya ce:
''Suna amfani da kungiyar CAN da kuma wasu cocina; sun je su na yada karya a kaina.
''Ina kalubalantar kowa ciki har da El-Rufai da Uba Sani da gaba daya jam'iyyar PDP da su fito su bada hujjar inda muka taba haduwa, bare ma ayi maganar karbar kudi daga daya a cikinsu.
''Babban dalilin takarata shi ne in cika yancin da kundin tsarin mulki ya ba ni, in yi nasara a zabe in kuma yi shugabanci da zai zama abin misali ga al'ummar Jihar Kaduna in kuma cika alkawarina da alkawarin jam'iyyarmu mai albarka, jam'iyyar LP."
Jonathan ya shawarci yan siyasa gabanin zaben gwamna
A wani rahoton, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya shawarci yan siyasa su dena yin siyasar a-mutu ko-ayi-rai, yana mai cewa bai kamata su kashe wadanda suke son su mulka ba.
Jonathan ya bada wannan shawarar ne a jihar Bayelsa a garin Sampou yayin da ya tafi ta'aziyyar rasuwar mahaifiyin Gwamna Douye Diri na Bayelsa.
Asali: Legit.ng