Jam'iyyar NNPP a Kano Ta Zargi Hukumar DSS Da Hada Baki Da APC

Jam'iyyar NNPP a Kano Ta Zargi Hukumar DSS Da Hada Baki Da APC

  • Jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a jihar Kano tayi zargin ana haɗa baki da hukumar DSS domin bata matsala a zaɓen jihar
  • Jam'iyyar NNPP ɗin tayi wannan zargin ne ta hannun ɗan takarar sanatan ta Baffa Bichi
  • Baffa Bichi yace za su fito su gudanar da zanga-zangar lumana domin neman shugaban hukumar DSS na jihar ya gaggauta sauka daga muƙamin sa

Jihar Kano- Jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a jihar Kano tayi zargin cewa da hukumar tsaron farin kaya (DSS) take takara a zaɓen ranar Asabar, ba da jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ba.

Jam'iyyar tayi zargin cewa hukumar tana aiki tare da jam'iyyar APC mai mulki a jihar domin murɗe abinda mutane suke so, amma ba zata bari hakan ya cigaba da faruwa ba. Rahoton Daily Trust

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar Accord Party Ta Balle Daga Hadakarta Da Jam'iyyar Peter Obi, Ta Koma Bayan Gwamnan APC Mai Neman Tazarce

Bichi
Baffa Bichi Tare Da Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Facebook
Asali: UGC

Da yake magana a madadin jam'iyyar, ɗan takarar sanatan jam'iyyar, Baffa Bichi, yace magoya bayan za su gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna adawar su kan cigaba da barin shugaban hukumar kan muƙamin sa ba bisa ƙa'ida ba, wanda yayi zargin cewa tun wata 15 baya yakamata ace yayi ritaya.

Yace zanga-zangar itace kaɗai zaɓin da ya rage wa jam'iyyar domin suna da bayanin sirri kan cewa an bar shugaban DSS ɗin ne kan muƙamin sa domin ya taimakawa jam'iyyar APC mai mulki a zaɓe mai zuwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jam'iyyar ta kuma yi zargin cewa an shigo da wasu jami'an DSS na musamman cikin jihar inda aka ajiye su a otal da kuma wasu gidaje na musamman domin cimma wannan ƙuɗiri.

Jam'iyyar tace ya zata gudanar da zanga-zangar lumana domin neman shugaban hukumar DSS ɗin ya gaggauta yin ritaya.

Kara karanta wannan

"Muna Da Hujja" Jam'iyyar PDP Tace Ta Bankado Shirin Gwamnan APC Na Yin Magudi a Zaben Gwamna

Ya kuma ƙara zargin cewa gwamna Ganduje ne ya nemi a kawo Muhammad a matsayin shugaban hukumar a shekarar 2017, sannan shine kuma ya buƙaci da a bar shi kan muƙamin sa duk da lokacin ritayar sa yayi, wanda a cewar sa hakan ya nuna akwai wata ƙullalliya a ƙasa.

Bichi yace dukkanin zaɓaɓɓun sanatoci, ƴan majalisar wakilai da ƴan takarar jam'iyyar, za su fito su jagoranci zanga-zangar a ranar Alhamis, idan dai har ba shugaban ƙasa bane ya sanya baki DG ɗin DSS na ƙasa ya sanya darektan DSS na Kano yayi ritaya.

A ranar Alhamis dai hukumar DSS tayi gargaɗi kan yin zanga-zanga a jihar a lokacin da ta cafke wasu magoya bayan jam'iyyar NNPP masu yunƙurin tayar da hargitsi a jihar. Rahoton Blueprint

"Ina Da Dangantaka Mai Kyau Tsakani Na Da Kwankwaso", Ganduje

A wani labarin na daban kuma, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, yayi ƙarin haske kan dangantakar dake tsakanin sa da Kwankwaso.

Ganduje ya bayyana cewa duk da banbancin siyasa dake a tsakanin su, suna da kyakkyawar alaƙa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng