Bani da Jam'iyya a Yanzu, Ina Goyon Bayan Wanda Raina Ke So, Dogara
- Tsohon shugaban majalisar wakilan tarayya, Yakubu Dogara, ya ce ba shi da wata jam'iyya a yanzu
- Dogara, ya ce a baya ya goyi bayan Atiku Abubakar, yanzu kuma yana tare da ɗan takarar gwamnan APC
- Ya ce zai goyi bayan duk ɗan takarar da ya kwanta masa kuma a kowace jam'iyyar siyasa ya fito
Tsohon kakakin majalisar dokokin tarayya, Yakubu Dogara, ya ce ba ya tare da kowace jam'iyyar siyasa a yanzu amma yana goyon bayan 'yan takara daga kowace jam'iyya a babban zaben 2023.
Dogara, mai wakiltar mazaɓar Dass/Tafawa Balewa/Bogoro a majalisa, ya yi wannan furucin ne a Channels tv yayin hira a cikin shirin Politics Today ranar Laraba.
Ya ce a zahirin gaskiya goyon bayan da yake nuna wa 'yan takara a jam'iyyu daban-daban, ba yana nufin shi ɗan tsalle-tsalle bane kamar yadda wasu ke faɗa.
Yakubu Dogara na ɗaya daga cikin sanannun jagororin jam'iyyar APC gabanin zaɓen fidda ɗan takarar shugaban kasa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Dogara na cikin manyan na sahun gaba wajen yaƙar Tikitin Musulmi da Musulunci daga bisani ya ayyana goyon bayansa ga Atiku Abubakar maimakon Tinubu.
Bayan Haka Dogara ya yi hannun riga da kudirin tazarcen gwamnan Bauchi, Bala Muhammad, kana daga baya ya marawa ɗan takarar APC, Air Marshal Sadique Abubakar, baya, kamar yadda The Cable ta rahoto.
Wace jam'iyya Dogara ya shiga a yanzu?
Yayin da aka tambaye shi ranar Laraba cewa wace jam'iyya yake ciki tsakanin APC da PDP, Yakubu Dogara ya ce:
"Ina goyon bayan wasu yan takara ne amma bana cikin kowace jam'iyya a halin yanzu, ina goyon bayan yan takara. Kowa ya san na marawa Atiku baya kan dalilaina da tuni na faɗi kowa ya ji."
"Yanzu ina tare da Air Marshal Sadique Abubakar, wanda ke neman zama gwamnan Bauchi a PDP., ina da yan takara a majlisar dokokin jiha."
A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya Rantsar da Mutane 7 da Ya Naɗa Mukaman mambobin kwamitin ICPC
Bayanai sun tabbatar da cewa an rantsar da mutanen jim kaɗan gabanin fara taron majalisar zartaswar.
Mambobin kwamitin ICPC sun kam ranstuwar aiki ne bayan shugaban kasa ya amince da sake naɗa su a karo na 2.
Asali: Legit.ng