Abin da Ya Faru Tsakanina da INEC da Shekarau a Takarar Sanata a NNPP Inji Hanga
- Rufai Hanga ya ce INEC tayi kokarin ta ki karbarsa a matsayin ‘Dan takaran jam’iyyar NNPP a Kano
- Duk da jam’iyya ta bada sunansa, ‘dan siyasar ya ce an nemi a bar Sanata Ibrahim Shekarau ya yi takara
- Sanata Hanga ya ce hakan ya jawo suka shiga kotu da INEC, kuma su ka samu nasara kan hukumar
Abuja - Rufai Hanga wanda jagora ne a jam’iyyar NNPP, ya zanta da tashar Trust TV inda ya tabo batutuwan da suka shafi takararsa da nasaarsa a zaben 2023.
An kai ruwa rana kafin hukumar INEC ta cire Malam Ibrahim Shekarau, ta maye gurbinsa da Rufai Hanga a matsayin zababben Sanata na tsakiyar Kano.
Sanata Rufai Hanga ya ce hukumar INEC ta ba shi mamaki domin dokar zabe ta ce idan ‘dan takara ya mutu ko ya bar jam’iyya ko ya janye, a maye gurbinsa.
Abin da ya faru a Kano ta tsakiya shi ne Ibrahim Shekarau ya bar NNPP ya kuma sanar da ya fasa takara, Hanga ya ce sai jam’iyya ta bada sunansa a madadi.
Shekaru ya kira Hanga a waya
“Shekarau ya kira ni a waya, ya fada mani cewa yana ba ni shawara ka da in bata lokaci da kudi a banza domin shugaban jam’iyya ya ce ba zai canza shi ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Shugaban INEC na kasa ya ce ba zai maye gurbinsa ba, lallai shi ne zai zama ‘dan takara."
- Rufai Hanga
An je kotu sau uku babu nasara
Bayan abin ya kai ga haka ne sai ‘dan siyasar ya ce suka je kotun tarayya, kuma su ka yi nasara aka ba su gaskiya, amma sai hukumar INEC ta daukaka kara.
Da aka je kotun daukaka kara, Hanga ya shaidawa Trust TV cewa Alkalai sun ba jam’iyyar NNPP gaskiya, suka ce dokar zabe ta sha gaban ka’idojin INEC.
"Sai suka sake daukaka kara zuwa kotun koli, a nan ma suka sha kasa a kan wancan hujjar dai."
- Rufai Hanga
Hanga ya kafa tarihi a 2023
Har zuwa yanzu tsohon Gwamnan na Kano bai kira Hanga domin taya shi murna ba, amma ‘dan siyasar ya ce babu wani sabani tsakaninsa da ‘danuwansa.
Hanga ya kafa tarihin zama mutum na farko da ya wakilci Kano ta tsakiya sau biyu a majalisar dattawa, abin da tsofaffin gwamnoni biyu ba su iya yi ba.
Asali: Legit.ng