2023: Labour Party Ta Rasa Mambobi 3000 a Hannun PDP a Jihar Abia

2023: Labour Party Ta Rasa Mambobi 3000 a Hannun PDP a Jihar Abia

  • Sama da ƴaƴan jam'iyyar Labour Party (LP) 3,000, suka koma jami'iyyar PDP a jihar Abia ana dab da zaɓe
  • Masu sauya sheƙar sun zargi ɗan takarar gwamnan jam'iyyar a jihar, Alex Otti, da ƙin yarda su gan shi
  • Sun kuma bayyana cewa ɗan takarar gwamnan yana tayin rufa-rufa kan daga ainihin yankin da ya fito a jihar

Obingwa- Ƴaƴan jam'iyyar Labour Party LP), 3200 sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ƙananan hukumomin Obingwa da Isiala-Ngwa ta Kudu a jihar Abia.

The Guardian ta rahoto cewa a Obingwa, Hon. Maduka Akpulonu, shine ya jagoranci masu sauya sheƙar a makarantar firamaren Osusu Amaukwa, a gaban shugaban jam'iyyar PDP na mazaɓar PDP Elder Erondu U. Erondu Jnr, a ranar Talata 14 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar Accord Party Ta Balle Daga Hadakarta Da Jam'iyyar Peter Obi, Ta Koma Bayan Gwamnan APC Mai Neman Tazarce

Alex Otti
Alex Otti, Ɗan takarar gwamnan Labour Party na jihar Abia Hoto: Labour Party
Asali: UGC

A ƙaramar hukumar Isiala-Ngwa ta Kudu, tsaffin mambobin jam'iyyar LP, sun bayyana cewa sun sauya sheƙa ne saboda halin rashin son ganin mutane na ɗan takarar tsohuwar jam'iyyar su, Alez Otti, da yadda kwata-kwata baya ganuwa.

Masu sauya sheƙar sun kuma zargi Otti da girman kai sannan yaudarar cewa ya fito ne daga ƙaramar hukumar Isiala-Ngwa ta Kudu, alhalin kuwa ya fito ne daga ƙaramar hukumar Arochukwu ta jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban masu sauya sheƙar Onyedikachi Nkechinturu wanda ya fito daga ƙauyen Umuegoro, ya bayyama cewa:

“Mun yi aiki tuƙuru domin ganin jam'iyyar Labour Party tayi nasara a zaɓen shugaban ƙasa dana ƴan majalisun tarayya."
“Yanzu lokaci yayi da zamu yi aiki da dan takarar gwamnan da muke da ƙwarin guiwa cewa zai saurari koken al'umma, ya bamu lokacin sa sannan ya tabbatar da tsaro a jihar mu."

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Fito Fili, Asirin Waɗanda Suka Janyowa Atiku Rashin Nasara a Zaɓe Ya Tonu

Zaben Gwamnoni: Jam'iyyar Accord Party Ta Koma Bayan APC a Jihar Legas

A wani labarin na daban kuma, jam'iyyar Accord Party (AP) ta koma bayan jam'iyyar APC a jihar Legas.

Jam'iyyar ta AP ta ɓallo ne daga haɗakar da tayi da jam'iyyar Labour Party a zaɓen shugaban ƙasan da aka gudanar a makonnin baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng