Zaben Gwamnoni: Jerin Mata 24 Da Ke Neman Takara a Fadin Jihohin Najeriya

Zaben Gwamnoni: Jerin Mata 24 Da Ke Neman Takara a Fadin Jihohin Najeriya

Za a gudanar da zaben gwamnoni a fadin jihohi 28 cikin 36 da ke Najeriya a ranar Asabar, 18 ga watan Maris. Akalla mata guda 24 ne za su fafata da takwarorinsu maza wajen neman kujerun gwamnoni a sassa daban-daban na kasar.

Legit.ng ta lura cewa yawan mata masu shiga harkar siyasa na kara karuwa a Najeriya musamman ma a zaben 2023.

Jam’iyyun siyasa 18 ne za su gabatar da yan takara a zaben amma mata biyu ne kawai suka lashe tikitin manyan jam’iyyun siyasa uku da suka hada APC mai mulki, babbar jam’iyyar adawa ta PDP da kuma sabuwar jam’iyyar matasa ta Labour Party.

Binani
Zaben Gwamnoni: Jerin Mata 24 Da Ke Neman Takara a Fadin Jihohin Najeriya
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai wacce ta fi shahara cikin yan takara 24 mata da ke neman kujerar gwamna a ranar Asabar ita ce Aishatu Dahiru Binani, wacce ke rike da tutar APC a jihar Adamawa.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC ta Kunshe Biliyoyin Kudi Wajen Saida Fam Ga Masu Sha’awar Takara

Ga cikakkun jerin mata 24 da ke neman kujerar gwamna a zaben

  1. Aishatu Dahiru Binani – APC a jihar Adamawa
  2. Gladys Johnson-Ogbuneke - SDP a jihar Abia
  3. Lancaster Okoro – PRP a jihar Abia
  4. Ekanem Abasiekeme - AA a jihar Akwa Ibom
  5. Udoh Emem Monday - SDP. a jihar Akwa Ibom
  6. Roseline Chenge - ADP a jihar Benue
  7. Aondona Dabo-Adzuana - ZLP a jihar Benue
  8. Abubakar Fatima - ADP a jihar Borno
  9. Ibiang Marikana Stanley - ADP a Cross River
  10. Onokiti Helen Agboola - Accord a jihar Delta
  11. Cosmas Annabel – APP a jihar Delta
  12. Chinenye Igwe - APM a jihar Ebonyi
  13. Ogochukwu Nweze - SDP a jihar Enugu
  14. Umar Binta Yahaya - AA a jihar Jigawa
  15. Yakubu Furera Ahmad - BP a jihar Kano
  16. Mahmud Aisha – NRM a jihar Kano
  17. Motunrayo Jaiyeola – APM a jihar Kwara
  18. Funmilayo Kupoliyi - APM a jihar Lagas
  19. Roseline Adeyemi - APP a jihar Lagas
  20. Patricia Tsakpa - ADP a jihar Nasarawa
  21. Khadijah Abdullahi-Iya - APGA a jihar Neja
  22. Aduragbemi Euba - YPP a jihar Oyo
  23. Beatrice Itubo - LP a jihar Rivers
  24. Hadiza Usman - ZLP a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Yadda Rikicin 'Yan PDP da Gwamna a Arewa Suka Jawo Fasto Ya Ci Zaben Gwamna

Jerin jihohi 15 da PDP ka iya lashewa a zaben gwamnoni na 2023

A wani labarin kuma, mun kawo cewa hasashe sun nuna cewa jam'iyyar PDP mai adawa a kasar ka iya nasara wajen kaso kujeru 15 a zaben gwamnoni da za a yi a ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng