Zaben Shugaban Kasa: Shehu Sani Ya Bayyana Abin Da Ya Kamata Shugaban Amurka Biden Ya Yi Wa Tinubu
- Tsohon dan majalisa daga jihar Kaduna, Sanata Shehu Sani, yana son shugaban Amurka Joe Biden ya taya zababben shugaban Najeriya Bola Tinubu murna
- A wani rubutu na raha da ya aka san shi da yi, Sani ya ce kamata nan take Biden 'ya aika sakon taya murna ta WhatsApp' ga Tinubu
- Jigon na PDP, amma ya ce shugaban na Amurka na iya amfani da 'sakon WhatsApp mai goge kansa' saboda abin da ka iya zuwa ya dawo
Sanata Shehu sani, tsohon dan majalisa kuma jigo a jam'iyyar hamayya ta Peoples Democratic Party, PDP, ya shawarci shugaban Amurka, Joe Biden, 'ya aika sakon taya murna ta WhatsApp' ga Bola Tinubu, zababben shugaban Najeriya.
Sani ya bada wannan shawarar ne rubutu na raha da ya yi a Twitter da Legit.ng ya gani a ranar Talata, 14 ga watan Maris.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jigon na PDP, amma, ya kara da cewa shugaban na Amurka ya yi amfani da 'sakon WhatsApp mai goge kansa', yana nufin ta yi wa a soke nasarar Tinubu a kotun sauraron karar zabe.
Jigon na PDP ya ce:
"Shawara ta ga Shugaba Biden shine ya tura sakon taya murna ga zababben shugaba Jagaban ta WhatsApp.
"Ko mai ke faruwa, shine zababben shugaban kasa. Biden na iya latsa sako mai goge kansa saboda abin da ka iya faruwa."
Shugabannin kasashen duniya sun taya Tinubu murna?
Tun bayan lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu da ake cece-kuce a kai, shugabannin kasashen duniya ciki har da Farai Ministan Birtaniya, Rishi Sunak, sun taya Tinubu murna.
Yayin da Legit.ng ba za ta iya tabbatarwa idan Shugaba Biden ya taya zababben shugaban kasar na Amurka ya taya Tinubu murna ba, gwamnatin Amurkan ta fitar da sanarwa kan zaben.
Mai magana da yawun hukumar kasashen waje na Amurka, Ned Price ya fitar da sanarwa yana cewa:
"Amurka na taya mutanen Najeriya, zababben shugaban kasa, da dukkan shugabannin siyasa biyo bayan ayyana sakamakon zabe da Hukumar Zaben Shugaban Kasa, INEC, ta yi na zaben ranar 25 ga watan Fabrairu."
Jigon APC Ya Yi Ikirarin Cewa IPOB Ta Yi Wa Peter Obi A Zaben Shugaban Kasa
Wani jigon jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar Legas, Biodun Ajiboye, ya yi ikirarin cewa kungiyar maso neman kafa kasar Biyafara, IPOB, sun yi wa Peter Obi aiki a zaben shugaban kasa.
Ajiboye ya yi ikirarin cewa Peter Obi bai taba fitowa karara ya soki mambobin haramtacciyar kungiyar ta IPOB ba.
Asali: Legit.ng