Doguwa, Wase da ‘Yan Majalisa 5 a Arewa Sun Kwallafa Rai Kan Kujerar Gbajabiamila

Doguwa, Wase da ‘Yan Majalisa 5 a Arewa Sun Kwallafa Rai Kan Kujerar Gbajabiamila

  • Zuwa yanzu, INEC ta tabbatar da cewa APC ta na da kujeru 162 a Majalisar Wakilan Tarayya
  • Labour Party (LP) da the New Nigeria People’s Party (NNPP) su na da ‘Yan majalisa 34 da 18
  • Jam’iyyun SDP, ADC da YPP suna da wakilcin mutum daya a Majalisa daga zaben 2023 da aka yi

Abuja - Tun da aka rabawa zababbun ‘yan majalisa takardun shaidar lashe zaben 2023, lissafi ya koma game da yadda za a raba mukamai da kujeru.

An bayyana cewa an fara samun wadanda suka fito su ka nuna su na sha’awar samun kujerar shugabancin majalisar wakilai.

Akwai ‘yan majalisa kimanin bakwai da alamu suka nuna za su so su gaji Femi Gbajabiamila wanda da wahala ya cigaba da zama shugaban majalisa.

Rt. Hon. Femi Gbajabiamila zai rasa kujerarsa ne domin ya fito daga Kudu maso yamma, yankin da shugaban kasa mai jiran gado, Bola Tinubu ya fito.

Kara karanta wannan

Jerin Duka Shugabannin PDP 9 da Aka Yi Rabuwar Tsiya da Su Daga 1999 zuwa 2023

Masu neman kujera ta #4 a kasa

A cikin wadanda suke sha’awar kujerar shugabancin, akwai Benjamin Kalu (APC, Abia) wanda shi ne mai magana da yawun ‘yan majalisar tarayya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hon. Idris Wase (APC, Filato) wanda shi ne mataimakin shugaban majalisar wakilan zai so ya samu cigaba, ya dare kujerar da ya rasa a wancan karo.

‘Yan Majalisa
Doguwa, Wase da Betara Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Aminu Jaji (APC, Zamfara) wanda ya dawo majalisar Najeriya bayan shekaru hudu yana gida tare da 'yan takaran APC a 2019, yana neman kujerar.

Watakila Muktar Aliyu Betara (APC, Borno) wanda yana cikin dadaddun ‘yan majalisan Arewa maso gabas ya shiga takaran idan an kai yankinsu.

Sannan akwai shugaban masu rinjaye, Alhassan Ado Doguwa (APC, Kano) sai dai har yanzu ba a tabbatar masa da kujerarsa ba, kuma ana shari’a da shi.

Babu mamaki APC ta kai kujerar zuwa Kudu maso gabas ko Arewa maso yamma. Idan aka yi haka, Hon. Benjamin Kalu zai iya samun mukamin.

Kara karanta wannan

Toh fa: Sanata ya ba da shawarin a ba Buhari wata babbar kujera a Najeriya bayan mika mulki

Hon. Wase wanda yake Arewa ta tsakiya zai yi fatan daga yankinsa za a fito da shugaban majalisa.

Takarar Hon. Abbas Tajudeen

Daga Arewa maso Yamma, an ji labari Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai yana goyon bayan shugabancin majalisa ya fada hannun Abbas Tajudeen.

Hon. Abbas Tajudeen ya yi nasarar komawa majalisar wakilan tarayya a karkashin jam’iyyar APC domin wakiltar mutanen Zariya a karo na hudu a jere.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng