Bago VS Kantigi: Muhimman Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Manyan Yan Takara 2 a Jihar Neja
A ranar Asabar, 18 ga watan Maris za a gwabza tsakanin jam’iyyun siyasa a zaben gwamnoni a fadin jihohin Najeriya guda 28 cikin 36.
Al’ummar jihar Neja da ke arewa ta tsakiya za su fito su zabi wanda suke so ya shugabance su a matsayin gwamna na tsawon shekaru hudu masu zuwa
A wannan fage, Legit.ng Hausa ta zakulo maku wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku sani game da manyan yan takarar gwamna a jihar Neja.
Muhammad Umar Bago shine dan takara karkashin inuwar jam’iyyar APC yayin da Isah Liman Kantigi shine ke rike da tutar PDP.
Muhammad Umar Bago na APC
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
- An haifi Hon. Mohammed Umaru Bago a garin Minna, babban birnin jihar Neja a ranar 22 ga watan Fabrairun 1974 a cikin kabilar Nupe.
- Mahaifinsa, Marigayi Alhaji Muhammad Mustapha (Baraden Nupe), TECHNO ya fito ne daga tsatson gidan sarauta na Masaba da ke garin Bida.
- Mahaifiyarsa Marigayiya Hajiya Aisha Mohammed ta fito daga gidan sarautar Jantabo da ke Lapai.
- Ya fara karatunsa makarantar Firamare na Marafa da ke garin Minna inda ya mallaki satifiket dinsa na farko a 1985 daga nan ya tafi kwalejin tarayya da ke Jos inda ya yi WAEC a 1991.
- Bago ya halarci jami’ar Usman Dan Fodio da ke jihar Sokoto inda ya mallaki digiri a bangaren kimiyyar siyasa. Ya kuma yi digiri na biyu a bangarori daban-daban.
- Bago ya yi dan majalisar wakilai mai wakiltan mazabar Chanchaga ta jihar Neja har sau uku.
- A yanzu haka, shine dan takarar gwamnan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Neja a zaben 2023.
Isah Liman Kantigi na PDP
- An haifi Hon. Isah Liman Kantigi a karamar hukumar Enagi da ke jihar Neja.
- Kantigi shine dan takarar gwamnan jihar Neja karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2023.
- Kantigi ya kasance tsohon kwamishinan kananan hukumomida harkokin sarauta na jihar Neja har sau biyu, jaridar Sun ta rahoto.
- A zaben 2015, Isah Kantigi aka tsayar a matsayin dan takarar mataimakin gwamna karkashin jam’iyyar PDP.
- Ya yi ciyaman na karamar hukumar Edati sau daya ya kuma yi shugaban kungiyar ALGON.
Zaben gwamna: Jam'iyyun siyasa 10 sun yi maja da PDP a jihar Ogun
A wani labari na daban, jam'iyyar PDP reshen jihar Ogun ta bayyana cewa jam'iyyun siyasa 10 da wasu fusatattun 'ya'yan APC sun dawo cikinta gabannin zaben gwamna na ranar 18 ga watan Maris.
Asali: Legit.ng