Rikicin Cikin Gida Ya Kudundune APC, PDP Daf da Zaben Gwamnoni a Jihohi 12
- Kusan mako guda ya rage a shirya zaben Gwamnoni da ‘yan majalisar dokoki na jihohi a Najeriya
- Amma ana ta fama da rikicin siyasa tsakanin jagororin jam’iyya da masu takarar Gwamnoni a 2023
- Babu zaman lafiya a Bauchi, Abia, Enugu, Oyo, Ribas, Edo, Katsina, Ekiti, Delta, Kwara da Benuwai
Abuja - A wani dogon rahoto da aka samu a Vanguard, an fahimci cewa rigingimun cikin gida sun yi kamari yanzu a manyan jam’iyyu na PDP da APC.
Akwai inda kusoshin jam’iyya suke goyon bayan ‘yan takaran wasu jam’iyya ko makamancin haka, wannan ya samo asali daga zaben tsaida gwani.
Jihohin da ake zargin ‘ya ‘yan Jam’iyya da shirya zagon-kasa su ne: Ogun, Bauchi, Abia, Enugu, Oyo, Ribas, Edo, Katsina, Ekiti, Delta, Kwara da Benuwai.
Sunday Vanguard ta ce wasu daga cikin ‘Yan PDP ko APC a wadannan jihohi za su yi wa abokan adawarsu aiki a zaben Gwamnoni da ‘yan majalisun jiha.
A jihar Bauchi, Rt. Hon. Yakubu Dogara yana goyon bayan ‘dan takaran APC, Sadiq Abubakar ya doke Gwamna Bala Mohammed na jam’iyyarsa ta PDP.
A maimakon ya goyi bayan jam’iyyarsa ta APC, Sanata Orji Uzor Kalu yana marawa kaninsa baya, yana so Mascot Kalu ya zama Gwamna a jam’iyyar APP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bauchi, Oyo da sauransu
Jam’iyyar PDP ta kori Chimaroke Nnamani sannan ta hana shi takarar Sanata a Enugu, dalili kuwa ya goyi bayan Bola Tinubu a kan Atiku Abubakar.
A dalilin rikicin G5, irinsu Jumoke Akinjide, Wole Oyelese, Hazeem Gbolarumi, Femi Babalola ba su goyon bayan Seyi Makinde ya zarce a zaben jihar Oyo.
Gwamna Nyesom Wike zai so Siminalayi Fubara ya zama magajinsa, amma akwai masu jin haushinsa a PDP saboda ya goyi bayan takarar Bola Tinubu.
Dan Orbih bai tare da Gwamna Godwin Obaseki a Edo tun ba yau ba, watakila rikicin nan zai yi tasiri a mako mai zuwa wajen zaben ‘yan majalisar dokoki.
Akwai ‘Yan PDP da ke fada da Yakubu Lado Danmarke a Katsina, a gefe Gwamna yana ta korar wadanda ake zargi sun ci amanar APC a babban zabe.
Rikicin tsakanin yaran Fayose da magoya bayan Atiku ne a zaben ‘yan majalisun dokokin Ekiti.
A Delta ma ana zargin mutanen James Ibori ba za su goyi bayan Sheriff Oborevwori ba, za su iya taimakawa Ovie Omo-Age mai neman Gwmana a APC.
Yadda Lai Mohammed ke rikici da Abdulrahaman Abdulrazaq a Kwara, haka lamarin yake a Benuwai, wasu za su ki zaben mutumin Samuel Ortom.
Ibikunle Amosun v Abiodun
A jihar Ogun, ana da labari Ibikunle Amosun da mutanensa ba su goyon bayan tazarcen Gwamna Dapo Abiodun, su na tare ne da Biyi Otegbeye na ADC.
Sanata Amosun ya fadawa magoya bayansa su zabi Jam’iyyar African Democratic Congress.
Asali: Legit.ng