Peter Obi Ya Tabbatarwa 'Obidients' Cewa Zai Kwato Musu Nasararsu, Bidiyo Ya Fito
- Mr Peter Obi ya bawa magoya bayansa a dukkan duniya cewa ba zai yi kasa a gwiwa ba wurin kwato musu nasararsu
- Dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar Labour ya bada tabbacin ga wasu magoya bayansa a jihar Legas
- Obi ya furta hakan ne yayin ziyarar da ya kai wa Jennifer Efedi, wata mata wacce wasu da ake zargin yan daban siyasa suka raunta a Legas
Jihar Legas - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, Mr Peter Obi, ya bada tabbacin ba zai karaya ba kan kokarin kwato nasararsa da ya yi ikirarin an sace.
Obi ya bada tabbacin ne yayin ziyarar da ya kai wa Jennifer Efedi, matar da wasu da ake zargin yan daba ne suka kai wa hari a Legas, ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu (yayin zaben shugaban kasa da yan majalisu).
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya bada tabbacin ba zai taba bawa magoya bayansa kunya ba.
Hakan na cikin wani bidiyo ne da Legit.ng ta gani inda tsohon gwamnan na Anambra, ya ke bada amsa ga matar yayin da ta ke bukatar kada ya dena kokarin kwato nasarar mutane.
Mata da wani na mijin a cikin bidiyon sun ce:
"Mun gode, yallabai. Yallabai, muna kaunar ka, muna son ka da dukkan zuciyar mu."
Ta cigaba da cewa:
"Don Allah kada ka karaya."
Shi kuma Obi ya amsa da cewa:
"A'a, a'a, a'a!"
Kalli bidiyon a kasa:
Peter Obi, Jam'iyyar Labour da INEC, Tinubu da APC
Peter Obi da jam'iyyar Labour a halin yanzu suna kotu tare da hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, da zababben shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu.
A karar da aka gabatar gaban kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa na shekarar 2023, Obi ya zargi INEC da ayyana Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa ba bisa ka'ida ba da wasu korafe-korafen.
DSS ta cafke wasu jiga-jigan PDP 3 a Kaduna kan zargin 'shirin tada husuma' yayin zabe da ke tafe
A wani rahoton, yan sandan farin kaya na DSS sun kama mataimakin shugaban kwamitin yakin neman zaben dan takarar gwamnan Kaduna na jam'iyyar PDP, Sa'idu Adamu.
An kama shi tare da Talib Mohammed da El-Abbas Mohammed shugabannin matasan PDP kan zargin shirin tada rikici yayin zaben gwamna da yan majalisu.
Asali: Legit.ng