Jam'iyyar SDP Ta Koma Bayan Ɗan Takarar Gwamnan APC a Jihar Oyo
- Jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) ta nuna goyon bayan ta ga ɗan takarar gwamnan APC na jihar Oyo
- Jam'iyyar ta bayyana cewa ta koma baya ɗan takarar ne saboda tana da yaƙinin zai yi abin a zo a gani a jihar
- Sai dai jam'iyyar tayi ƙarin haske akan goyon bayan ɗan takarar, inda tace a kujerun ƴan majalisun jiha ba ta tare da APC
Jihar Oyo- Jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) a jihar Oyo ta marawa ɗan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Teslim Folarin, baya.
Shugaban jam'iyyar na jihar, Michael Okunlade, shine ya bayyana hakan a yayin wani taron gaggawa da yayi da shugabannin jam'iyyar na ƙananan hukumomi 33 na jihar. Rahoton The Cable
Shugaban jam'iyyar yace yana da ƙwarin guiwa sosai kan wannan haɗewar ta su da ɗan takarar gwamnan na jam'iyyar APC.
Okunlade yace jam'iyyar ta yanke shawarar marawa ɗan takarar APC baya ne saboda wasu abubuwa na rashin daidai da gwamnatin Seyi Makinde tayi musu a jihar. Rahoton Thisday
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Mun yi amanna cewa domin mu kawo sauyi a jihar nan akwai buƙatar mu yi haɗaka mai ƙarfi da jam'iyyar da za ta iya tumɓuke wannan gwamnatin wacce ta nuna bata da wasu abubuwa na cigaba."
Shugaban jam'iyyar ya bayyana cewa bayan sun gudanar da tarurruka da dama da ƙusoshin jam'iyyar sun yanke shawarar su marawa Folarin baya.
Sai dai, ya bayyana cewa goyon bayan su ya tsaya ne kawai a zaɓen gwamna, inda yayi kira da magoya bayan su da su zaɓi ƴan takarar jam'iyyar SDP a kujerun ƴan majalisar dokokin jihar.
“Mun yanke wannan hukuncin ne ba domin komai ba sai domin cigaban jihar mu. Shi ba irin mutanen nan bane da za suyi alƙwarin da ba za su iya cikawa ba."
Muhimman Abubuwan Sani Game Da Ƴan Takarar Gwamnan Borno 2
A wani rahoton, mun kawo muku muhimman abubuwan sani dangane da manyan ƴan takarar gwamnan jihar Borno guda biyu.
Takarar gwamnan jihar dai tafi zafi ne a tsakanin jam!iyyar APC da PDP.
Asali: Legit.ng