Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan PDP Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC a Jihar Neja
- Ana dab da zaɓen gwamna, jam'iyyar All Progressives Congress (APC) tayi babban kamu a jihar Neja
- Tsohon ɗan takarar gwamnan jam'iyyar PDP a jihar, Umar Nasko ya sauya sheƙa zuwa cikin ta
- Umar Nasko ya sha alwashin zage damtse wajen yin aiki tuƙuru domin tabbatar da nasarar jam'iyyar a zaɓen dake tafe
Jihar Neja- Tsohon ɗan takarar gwamnan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Neja, Umar Nasko, ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC), a ranar Alhamis. Rahoton Punch
Nasko wanda yayi takarar gwamnan jihar a shekarar 2015 da 2019, yasha kashi a hannun gwamna mai ci yanzu, Abubakar Bello.
Umar Nasko ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC a Minna, babban birnin jihar Neja.
Ya bayyana cewa ya yanke shawarar komawa APC ne bayan da ɗan takarar gwamnan jam'iyyar na jihar, Umar Bago, ya tuntuɓe shi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ce Bago ya neme shi da ya zo su haɗa hannu tare wajen ciyar da jihar gaba.
“Na koma jam'iyyar APC ne bayan da ƴan jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin ɗan takarar gwamna, Umar Bago, suka tuntuɓe ni." Inji shi
Ya bayyana cewa wannan ba ƙaramin cigaba bane ga jihar Neja sannan yayi alƙwarin yin aiki tuƙuru domin ganin jam'iyyar tayi nasara a zaɓen dake tafe.
“Wannan ba ƙaramar nasara ba ce ga ƴaƴan jam'iyyar a jihar Neja, sannan nayi alƙwarin zan yi aiki tuƙuru domin tabbatar da cewa APC tayi nasara a zaɓukan ranar 18 ga watan Maris."
Nasko yayi kira ga magoya bayan shi da su tabbatar cewa sun yiwa jam'iyyar APC domin cigaban ta.
“Ina kira ga dukkanin magoya bayana a jihar da su zage ɗamtse su yi aiki tukuru domin tabbatar da cewa jam'iyyar APC tayi nasara a ranar 18 ga watan Maris.
Umar Bago, wanda ya tarbi Nasko ya bayyana shi a matsayin wani babban kamu ga jam'iyya. Rahoton TVC News
Sakataren APC Ya Fadi Abin da Ya Taimaki Bola Tinubu, Ya Doke Atiku Abubakar da Obi
A wani labarin na daban kuma, wani babban jigo a jam'iyyar APC, ya bayyana abinda ya taimaki Bola Tinubu wajen yin nasara akan Atiku da Peter Obi.
Bola Tinubi dai ya samu nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa bayan ya kayar da waɗannan ƴan takarar biyu.
Asali: Legit.ng