“Ku Ma Kun Sha Kashi a Zaben Sanata”: Atiku Ya Caccaki Wike Da Sauran Gwamnonin G5
- An bukaci gwamnonin jam'iyyar PDP da ake kira da G5 da su guji yi wa Atiku Abubakar ba'a kan faduwa da ya yi a zabe
- Kakakin kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na PDP, Sanata Dino Melaye ne ya yi wannan kira
- Tsohon dan majalisar ya kuma ce yana da matukar muhimmanci gwamnonin G5 lura cewa mambobinsu ma sun fadi zaben sanata
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya yi wa gwamnonin G5 wankin babban bargo saboda murna da suke da faduwarsa a zaben da aka kammala.
Kakakin kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na PDP, Dino Melaye, ya gargadi gwamnonin kan cewa kada su yi murna da faduwar Atiku saboda su ma sun fadi zaben Sanata.
Melaye ya kuma bayyana cewa gwamnonin ba za su iya ikirarin sune suka sa Atiku ya fadi ba tun da suma sun gaza kai kansu ga nasara a zaben sanata, rahoton Sahara Reporters.
Dan siyasan na jihar Kogi ya dage cewa gwamnonin G5 basu da wani muhimmanci a zaben shugaban kasa da aka kammala, rahoton Vanguard.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A zaben shugaban kasa na 2023 da aka kammala kwanan nan, Atiku ne ya biyo bnayan tsohon gwamnan jihar Lagas, Bola Tinubu inda Peter Obi na Labour Party ya zo na uku.
Tun bayan ayyana sakamakon zaben shugaban kasar na 2023 da hukumar zabe ta kasa ta yi, gwamnonin G5 sun ci gaba da yin ba'a kan faduwar Atiku.
Uku cikin gwamnonin G5 sun nemi takarar sanata amma suka fadi
Gwamnonin G5 din sune Nyesom Wike na jihar Ribas, Okezie Ikpeazu na jihar Abia, Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu, Seyi Makinde na jihar Oyo da Samuel Ortom na jihar Benue.
Uku daga cikin gwamnonin sun fadi a zaben sanata, sai dai Makinde wanda ke neman zarcewa a karo na biyu da kuma Wike wanda bai nemi takarar kowace kujerar siyasa ba.
PDP ta zargi INEC da shirin goge bayanan da ke kan BVAS
A wani labari na daban, jam'iyyar PDP ta zargi hukumar zabe ta kasa, INEC, da kokarin shafe shaidar da take da ita wanda ke nuna lallai an yi magudi a zaben shugaban kasa na 2023.
Asali: Legit.ng