Obi Ya Soke Zuwa Kamfen Din Yan Takarar Gwamna, Yana Shirin Zuwa Kotu Ranar 8 Ga Watan Maris
- Peter Obi ya sanar da cewa zai rika zuwa kotu da kansa tare da lauyoyinsa don shari'ar zaben shugaban kasa na 2023
- Ana fatan kotun za ta yanke hukunci kan bukatar da INEC ta gabatar na sake daidaita na'urar BVAS
- Obi kuma ya sanar da soke shirin da ya yi a baya na zuwa jihohi don cigaba da kamfen din yan takarar gwamna
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, Peter Obi ya sanar da soke dukkan tafiye-tafiyen zuwa kamfen din yan takarar gwamna a jihohin kasar.
A wani rubutu da ya yi a Twitter, 8 ga watan Maris, Obi ya ce ya kamata ya fara zuwa kamfen din yan takarar gwamna da yan majalisar jihohi.
Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya ce a baya ya yi shirin zuwa jihohin Nasarawa, Legas, Enugu, Abia, Delta, Edo, Rivers, Plateau da Borno amma ya soke saboda yana shirin zuwa kotu don hukuncin bukatar da hukumar INEC ta yi na sake daidaita na'urar BVAS.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kalamansa:
"Ya kamata in fara kamfen din mu na yan takarar gwamnonin jihohi na jam'iyyar Labour da yan majalisun jiha yau. Da farko, na yi shirin zuwa jihohin Nasarawa, Legas, Enugu, Abia, Delta, Edo, Rivers, Plateau, Borno ds."
Obi ya bukaci Obidients su cigaba da kamfen a jihohi
Obi ya karfafawa magoya bayansa gwiwa su cigaba da kamfen na yan takarar gwamna a yayin da jam'iyyar ke neman hakkinta a kotu.
Kalamansa:
"A yayin da muke fafutikan ganin an bi doka, ina kira ga dukkan OBIdients a jihohi su cigaba da yi wa yan takarar mu kamfe, Gbadebo Rhodes Vivour a Legas, Chijoke Edeoga a Enugu, Patrick Dakum a Pleteau, Alex Otti a Abia, Ken Pela a Delta.
"Ibrahim Mshelia a Borno da sauransu. Yana kuma da muhimmanci Obidients su zabi yan takara masu cancanta, hali na gari, iya aiki da tausayi.
"Zan cigaba da jajircewa da kuma mayar da hankali sosai ga aikin mu na kwato nasararmu. Sabuwar Najeriya abu ne mai yiwuwa ne!"
Dalilin da yasa INEC ba ta tura sakamakon zabe zuwa matattaran bayanai na yanar gizo kai tsaye ba, Jigon APC
A wani rahoton, kun ji cewa Ekene Enefe, jigon jam'iyyar APC ya ce hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ba ta tura sakamakon zabe zuwa matattaran bayanai na yanar gizo bane saboda an dako masu kutse daga Isra'ila da Rasha don sauya sakamakon zaben.
Asali: Legit.ng