Bola Tinubu Ya Shiryawa PDP da LP, Ya Tanadi Lauyoyi 50 da Za Su Kare Shi a Kotun Zabe

Bola Tinubu Ya Shiryawa PDP da LP, Ya Tanadi Lauyoyi 50 da Za Su Kare Shi a Kotun Zabe

  • Wole Olanipekun wanda ya taba rike kungiyar NBA zai jagoranci Lauyoyin Bola Tinubu a kotun zabe
  • H. M. Liman, Yusuf Ali, Lateef Fagbemi da Ahmed Raji su na cikin Lauyoyin zababben shugaban kasar
  • Manyan lauyoyi 50 za su nemi su gamsar da kotu Tinubu ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi

Abuja - Fitaccen Lauyan nan, Wole Olanipekun da wasu abokan aikinsa 49 sun amince su tsayawa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a kotun karar zabe.

The Nation ta kawo rahoto cewa tsohon shugaban kungiyar Lauyoyin na kasa yana cikin bangaren masu kare nasarar ‘dan takaran APC a zaben 2023.

Lauyoyin su na sauraron tuhuma da korafi daga Atiku Abubakar da Peter Obi da suka nemi takarar shugabancin Najeriya tare da Bola Tinubu na APC.

‘Yan takaran jam’iyyun hamayyan PDP da LP sun kai kara a kotun sauraron korafin zabe, su na masu ikirarin an tafka magudi a zaben shugabancin kasa.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 9 da Jiga-Jigan Jam’iyyar PDP Za Su Taso INEC a Gaba a Kan Nasarar Tinubu

Lauyoyi za su fara shiri

Rahoton ya nuna Lauyoyin da za su tsayawa Tinubu za su yi zamansu na farko yau a Legas. A taron ne za a tattauna yadda za a tunkari PDP da LP.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Akwai yiwuwar wasu daga cikin Gwamnonin jihohin PDP su bada shaida a kotun zaben, su nuna ba ayi magudi a murdiya a zaben jihohinsu ba.

Bola Tinubu
Bola Tinubu a Fadar Rilwanu Akiolu Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Idan labarin da muka samu ya tabbata, wasu daga cikin manyan Lauyoyin nan da sun kai matsayin SAN, za su yi wa ‘dan takaran na APC aiki kyauta.

Wasu lauyoyin sun yi imanin cewa ba a taba yin zabe na gaskiya da adalci a Najeriya kamar wanda hukumar INEC ta shirya a ranar 25 ga Febrairu ba.

Sauran lauyoyin Tinubu a kotun zaben sun hada da tsohon Ministan shari’a, Akin Olujimi, Yusuf Ali, Lateef Fagbemi, A.U. Mustapha, da Ahmed Raji.

Kara karanta wannan

Zaben Jihohi: Gwamnoni da ‘Yan Takara 11 da Ke Cikin Dar-Dar Bayan Zaben Shugaban Kasa

Akwai lauyoyi irinsu Abiodun Owonikoko, Kemi Pinheiro, Niyi Akintola da H.M. Liman.

Jaridar ta kara da cewa ragowar su ne Taiwo Osipitan, Babatunde Ogala, Roland Otaru, James Onoja, Muiz Banire, Olusola Oke, da M. A Abubakar.

“Dole mulki ya koma Kudu" - Wike

A farkon makon nan ne aka samu labari cewa Gwamna Nyesom Wike ya ce da an saurari gargadin G5, da Bola Tinubu bai doke Atiku Abubakar ba.

Nyesom Wike ya sake nanata matsayarsa cewa dole sabon shugaban Najeriya ya zama ‘Dan Kudu domin shugabanci ya shekara takwas a Arewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng