'Yan Takarar Gwamna 7 Sun Koma Bayan Ɗan Takarar PDP a Jihar Kaduna
- Ana dab da a fara zaɓen gwamnoni a Najeriya, jam'iyyar PDP a jihar Kaduna tayi wani babban kamu
- Ƴan takarar gwamna mutum bakwai sun haƙura da takara sun marawa ɗan takarar PDP baya a jihar
- Ƴan takarar sun bayyana dalilan da ya sanya suka yanke wannan hukuncin na haƙura da takarar su
Jihar Kaduna- Ƴan takarar gwamna mutum bakwai a zaɓen gwamnan jihar Kaduna na ranar 11 ga watan Maris, 2023, sun koma bayan ɗan takarar gwamnan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Isah Muhammad Ashiru Kudan.
Ƴan takarar gwamnan sun fito ne daga jam'iyyun, Young Progressive Party (YPP), Action Alliance (AA), Allied People’s Movement (APM), Action People’s Party (APP), All Progressives Grand Alliance (APGA).
Sauran sun haɗa da National Rescue Movement (NRM) da Zenith Labour Party (ZLP). Rahoton Leadership
Shugaban ƙungiyar ƴan takarar mai suna ƙungiyar ƴan takarar ceto da sake gina Kaduna, Ambassador Sani Yaya, shine ya sanar da wannan matakin na su a birni Kaduna a ranar Litinin, yayin ganawa da ƴan jarida. Rahoton Within Nigeria
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Yau muna son mu sanar da goyon bayan mu da biyayyar mu ga Rt. Hon. Isah Muhammad Ashiru Kudan, ɗan takarar gwamnan jam'iyyar PDP." Inji shi
“Mun yanke wannan hukuncin ne bayan mun tattauna sosai da mambobin jam'iyyun mu da sauran al'ummar jihar Kaduna."
“Wannan matakin namu ya samu ne a dalilin burin mu na samun jiha ɗaya dunƙulalliya ba tare da la'akari da bambancin ƙabila ko addini ba, sannan muna da ƙwarin guiwar cewa Isah Ashiru Kudan,
"Shine ɗan takara ɗaya tilo da zai iya haɗa kan jihar nan."
"Hakan ya bayyana a yadda yayi kamfen ɗin sa wanda ya mayar da hankali wajen gina jihar Kaduna, da yadda ya zaɓo mataimakin sa domin bayar da wakilicin adalci ga Kiristoci da Musulmai waɗanda sune manyan jagorori a jihar."
“A yayin da wasu ƴan siyasa masu neman mulki ido rufe suka koma amfani da addini, Isah Ashiru ya zaɓi ya mayar da hankali kan abubuwan da suka damu al'ummar jihar kaɗai, da mutunta ɓangaren kowane addini."
"A bisa hakan, muke kira ga al'ummar jihar Kaduna da su fito ƙwan su da ƙwarƙwatar su a ranar 11 ga watan Maris, domin zaɓar Ashiru/Ayuba domin ciyar da jihar Kaduna gaba."
Da yake maraba da wannan goyon baya da suka bashi, Isah Ashiru Kudan, ya yabawa ƴan takarar gwamnan sannan ya tabbatar musu da cewa zai dama da si idan ya amshi mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Jam'iyyar APC Ta Karbi Dubbannin Masu Sauya Sheka a Jihar Gombe
A wani labarin na daban kuma, jam'iyyar APC ta samu dubunnan masu sauya sheƙa zuwa cikin ta a jihar Gombe.
Jam'iyyar APC dai ita ke riƙe da madafun iko a jihar Gombe.
Asali: Legit.ng